{"id":38998,"date":"2023-07-14T16:47:38","date_gmt":"2023-07-14T13:17:38","guid":{"rendered":"https:\/\/edutsn.com\/karatun-likitanci-a-iran\/"},"modified":"2024-02-29T10:37:06","modified_gmt":"2024-02-29T07:07:06","slug":"karatun-likitanci-a-iran","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/karatun-likitanci-a-iran\/","title":{"rendered":"Karatun likitanci a Iran"},"content":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_38998\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"38998\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" =0 title=\"\"><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div><p>Karanta kwas \u0257in likitanci shi ne burin mafi yawan matasa masu karatu. Kwas \u0257in likitanci \u0257aya ne daga cikin kwasa-kwasai masu riba sosai wanda duk shekara yana jan hankalin \u0257alibai masu yawa zuwa gare shi. Ku kasance tare da mu a wannan rubutun domin samun cikakkiyar gabatarwa a kan karatun likitanci a Iran.<\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Tarihin_likitanci_a_Iran\"><\/span>Tarihin likitanci a Iran<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>An fara karatun likitanci a Iran ne a shekara ta 1851 miladiyya a Darul Funun. Daga shekarar 1928, karatun likitanci a Iran ya samarwa kansa tsari na musamman. A 1934, An kirkiro wata sabuwar hanya ta musamman don karatun likitanci a Iran, ta hanyar assasa makarantar likitanci a Jami&#8217;ar Tehran. Makarantun likitanci na Shiraz, Isfahan da Tabriz a shekarar 1946, bayan shekaru uku; a 1949, Makarantar Kiwon Lafiya ta Mashhad ta fara aiki. Kwalejin kimiyyar kiwon lafiya ta \u0199asa (Shahid Beheshti ta yanzu), Ahvaz, Soja, Shahshahi (Iran ta yanzu), Kermanshah, Sari, Hamadan, Urmia, Kerman, Jahrom da Fasa an kafa su kafin juyin juya halin Musulunci.<\/p>\r\n<p>Bayan nasarar juyin juya halin musulunci na Iran da kuma sauyin tsarin ma&#8217;aikatu, a shekarar 1986, an \u0253am\u0253are \u0199ungiyar koyar da ilimin likitanci daga ma&#8217;aikatar kimiyya da ilimi ta gaba da sakandare, inda ta ci gaba da aiki tare da ma&#8217;aikatar lafiya da sunan; Ma&#8217;aikatar Lafiya, Jiyya da Ilimin Likitanci.<\/p>\r\n<h2><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-35450 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/07\/%D9%BE%D8%B2%D8%B4%DA%A9%DB%8C-%D8%AF%D8%B1-%D8%A7%DB%8C%D8%B1%D8%A7%D9%86.jpg\" alt=\"Karatun likitanci a Iran\" width=\"700\" height=\"619\" title=\"\"><\/h2>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Gabatar_da_daurorin_karatun_likitanci_a_Iran\"><\/span>Gabatar da daurorin karatun likitanci a Iran<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>Duka daurorin karatun likitanci a Iran bisa al&#8217;ada zangon karatu 14 ko 15 ne, idan babu shara\u0257in da ya gifta, amma tun yanzu ya kamata mu san cewa a fagen karatun likitanci, a na amfani da kalmar &#8216;daura&#8217; ne a maimakon kalmar &#8216;zango&#8217;. A jumlace, tsawon lokacin karatun kwasa \u0257in likitanci, kamar kwas \u0257in General Medicine, shekara 8 zuwa 9 ne. Specialization na likitanci kuma ya na \u0257aukar a\u0199alla shekara 4 (ya danganci fannin da za a karanta). A babin \u0199arin bayani, za mu fara kawo muku matakan karatun wannan kwas (na likitanci). Matakan karatun wannan kwas \u0257in daurori ne guda 4 kamar haka:<\/p>\r\n<ol>\r\n\t<li><strong>Basic Sciences<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Physiopathology<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Clinical Internship<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Clinical Internship (virtual)<\/strong><\/li>\r\n<\/ol>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Daurar_Farko_Basic_Sciences\"><\/span>Daurar Farko: Basic Sciences<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>Daura ta farko a kwas \u0257in na Genera Medicine, ita ce daurar Basic Sciences. Daurar a bisa al&#8217;ada, a na koya wa \u0257alibai ne a mataki na farko mai tsawon shekara 2. A cikin wannan kwas \u0257alibai na samun masaniya a kan darusan farko na likitanci. A cikin wannan kwas, yawancin lokuta a kan ba da tsarin darussa ga sababbin \u0257alibai. Bayan \u0257alibai sun kammala zangon karatu 4, za su zana jarabawar gwaji domin wucewa daura ta gaba. Daurar Basic Sciences, \u0257aya ce daga cikin daurori mafi muhimmanci a kwas \u0257in likitanci domin a nan ne \u0257alibai ke sanin asasi da tushen jikin \u018aan Adam da yanayinsa. Bayan \u0257alibai sun yi wannan daurar kuma sun yi jarabawar gwaji, za su wuce daurar Physiopathology.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Daura_ta_biyu_Physiopathology\"><\/span>Daura ta biyu: Physiopathology<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>Daura (mataki) ta biyu a kwas \u0257in likitanci, ita ce daurar physiopathology. Bisa al&#8217;ada wannan daurar ta shekara 1 ce kuma tana da zango 6 zuwa 7. A wannan daurar ne ake gabatar ma \u0257alibai da darussan Physiology da Pharmacology. Bisa al&#8217;ada ana gabatar da jarabawar wannan daura ne duk bayan wata 1. A wannan daurar \u0257alibai ke sanin cikakken tsari da nau&#8217;o&#8217;in cutukan jiki. Bayan \u0257alibai sun kammala wannan daura, za su shiga daura ta 3 da kuma asibitoci. Daura ta uku ita ce Daurar Internship.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Daura_ta_uku_Clinical_Internship_Strategy\"><\/span>Daura ta uku: Clinical Internship (Strategy)<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>Daura ta uku wadda ake kira da Internship, ita ke shigar da \u0257alibai a harabar asibitoci. Wannan daurar ta shekara 2 ce kuma tana da zango 4 zuwa 5. Daurar ta kasu kashi biyu, theory da practical. A cikin wannan daura, \u0257alibi yana aiki a matsayin mai gadi tsawon wasu ayyanannun sa&#8217;o&#8217;i na dare. Daurar internship na taimaka ma \u0257alibi wurin koyon abubuwan da ya karanta a aikace. Bayan \u0257alibai sun kammala wannan daura, su na yin wata jarabawar gwajin pre-internship. Cin wannan jarrabawar shi ne lasisin shiga daurar horon asibiti.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Daura_ta_hu%C9%97u_Clinical_Internship_Internship\"><\/span>Daura ta hu\u0257u: Clinical Internship (Internship)<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>Daurar \u0199arshe ta karatun likitanci ita ce daurar horon asibiti (internship). Daurar ta shekara 2 ce kuma gaba\u0257ayanta a asibiti ake yin ta. Ayyukan \u0257alibai a wannan daurar za su kasance a \u0199ar\u0199ashin kulawar malamai. Clinical internship ita ce daura mafi wahala a likitanci, saboda \u0257alibai za su yi mu&#8217;amala ne kai-tsaye da marasa lafiya. Idan \u0257alibai su ka yi nasarar tsallake wannan daurar, kuma su ka ci jarabawarta, shi kenan za a gabatar da su a matsayin likitoci a dokance.<\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"i\"><\/span>\u00a0<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<h2><strong><img decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-35462 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/07\/%D9%BE%D8%B2%D8%B4%DA%A9%DB%8C-%D8%AF%D8%B1-%D8%A7%DB%8C%D8%B1%D8%A7%D9%86-4.jpg\" alt=\"Karatun kwas \u0257in likitanci a Iran\" width=\"700\" height=\"495\" title=\"\"><\/strong><\/h2>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Kwas_%C9%97in_likitanci_shekara_nawa_ne\"><\/span>Kwas \u0257in likitanci shekara nawa ne?<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>\u018aaya daga cikin abubuwan da su ka \u0199ara ma karatun likitanci wahala, shi ne tsawon lokacin da ake \u0257auka kafin a kammala. Tsawon lokacin karatun likitanci ya \u0257ara na sauran kwasa-kwasai sosai idan an kwatanta. Wannan ya na nufin cewa masu sha&#8217;awar karanta wannan kwas su sani cewa, karatun likitanci na \u0257aukar shekara 8 kafin a kammala. Masu sha&#8217;awar kwas \u0257in, bayan sun kammala shekarunsu 8 na karatu, za su iya zuwa su yi jarabawar residency domin kar\u0253ar shaida. Me yiwuwa da yawa su so sanin cewa meye tsawon lokacin da ake \u0257auka kafin a samu gogewa a likitanci? Ga \u0257aliban da ke bu\u0199atar kar\u0253ar shaidar gogewa, dole ne su \u0199ara a\u0199alla shekara 4 don cigaba da karatunsu. A sau\u0199a\u0199e za a iya cewa domin samun wannan shaidar, za a bu\u0199aci shekara 12 na karatu.<\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Kwasa-Kwasan_likitanci_mafi_kyawu_a_Iran\"><\/span>Kwasa-Kwasan likitanci mafi kyawu a Iran<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>Akwai kwasa-kwasan likitanci masu yawa wa\u0257anda ake so. Masu sha&#8217;awar likitanci su kan fifita bada lokacinsu domin karantar wa\u0257annan kwasa-kwasan na likitanci. A \u0199asa, za mu kawo muku mafi kyawun kwasa-kwasan likitanci daga mahangar \u0257aliban likitanci.<\/p>\r\n<ol>\r\n\t<li><strong>Pharmacology<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Nursing<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Midwifery<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Dentistry<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Veterinary Medicine<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Anesthesiology<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Physiotherapy<\/strong><\/li>\r\n<\/ol>\r\n<h2><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-35470 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/07\/%D9%BE%D8%B2%D8%B4%DA%A9%DB%8C-%D8%AF%D8%B1-%D8%A7%DB%8C%D8%B1%D8%A7%D9%86-6.jpg\" alt=\"Jami&#039;o&#039;in likitanci a Iran\" width=\"700\" height=\"467\" title=\"\"><\/h2>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Gabatar_da_rassan_karatun_likitanci_a_Iran\"><\/span>Gabatar da rassan karatun likitanci a Iran<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>Likitanci yana da kwasa-kwasai masu yawa wanda idan muna so mu fa\u0257i mafi shahara daga rassan likitanci a jimla \u0257aya, sai mu ce:<\/p>\r\n<ul>\r\n\t<li><strong>Internal Specialization:<\/strong> A wannan fannin, likita yana da fahimtar gane cuta da magance ta. Wazifar likitan cikin gida ita ce, gano cuta, da magance matsalolin asibiti na marasa lafiya. Ko da yake a wasu lokuta yakan bar ma abokan aikinsa ayyukan da suka shafi tiyata.<\/li>\r\n\t<li>\r\n<p dir=\"rtl\"><strong>Specialization of General Surgery:<\/strong> A baya, General Surgeons (likitocin fida) sun kasance su na yin ayyukan orthopedics, urology, da sauransu, amma bayan samar da specializations daban-daban na likitanci, aikinsu ya takaitu zuwa tuyatar gastrointestinal da thyroid, tiyatar sauran sassan jiki kuma aka barma specializations na sama.<\/p>\r\n<\/li>\r\n\t<li><strong>Anesthesiologist:<\/strong> Wadannan kwararrun suna rubuta magungunan da a ke bukata ne wurin kashe zafi ko kawar da hayyaci lokacin aikin tiyata, haihuwa da sauransu. Kuma su na duba alamomin rayuwa na maras lafiya a lokacin da ba ya cikin hayyacinsa. hakazalika, su na tafiyarda al&#8217;amuran emergency na asibiti, kamar irin su tsayawar zuciya, ko daukewar numfashi kwatsam.<\/li>\r\n\t<li><strong>Neurosurgery Specialty:<\/strong> Tiyatar kwakwalwa, lakka, warkar da bugawar kwakwalwa da tumor na kwakwalwa da lakka, ya ta&#8217;allaka ne da wannan sashen.<\/li>\r\n\t<li>Obstetrics and Gynecology Surgeon: Ganowa, magani da ayyukan tiyatar da su ka shafi mata a lokacin da su ke dauke da juna biyu da lokacin nakuda, da kuma rashin haihuwa, sun ta&#8217;allaka ne da wannan sashe na likitoci.<\/li>\r\n\t<li><strong>Nutritional Expertise:<\/strong> Wadannan mutanen su kuma, sun kware a aikin ciyarwa da daidaita abincin mutane, kuma su na bada shawara a kan abincin mara lafiya bayan sun yi la&#8217;akari da yanayinsa (misali rashin cin abinci) da bukatunsa. Daliban da ke sha&#8217;awar yin karatu a wannan fannin dole ne su kammala digiri na likitanci, kuma su sami lasisin da suka dace don ganowa da magance matsalar cin abinci.<\/li>\r\n\t<li>Specialization of Ear, Throat and Nose Surgery (Ear Nasal ENT): Ganowa, magani da tiyatar kunne, haba, fuska, hanci da tonsils sune ayyukan wa\u0257annan likitocin. Koda yake, ayyukan da su ka kebanci hakori yawanci likitan hakori ne ke yin su.<\/li>\r\n\t<li><strong>Pediatricians:<\/strong> Likitocin yara: Sun kware wajen kula da mutane masu karancin shekaru, tun daga kan jarirai har zuwa \u2019yan shekara 18, wasu lokuta kuma har zuwa 21. Wa\u0257annan \u0199wararrun suna ba da kulawa ta farko kamar alluran rigakafi, tantance yara, duba lafiyar \u0257alibai, da magance mura. Yakamata a rika tura wasu cututtuka masu tsanani da rikitarwa zuwa ga likitan yara don su samu kulawa ta musamman. Wasu likitocin yara sun \u0199ware a wuraren da suka shafi shekarun jarinta, cin zarafin yara, da al&#8217;amuran da ke shafar girman yara kamar su Autism, rashin lafiyar halayyya, da Down syndrome.<\/li>\r\n\t<li><strong>Radiology Specialty:<\/strong> Tare da bunkasar fasaha a cikin harkar likitanci da kuma amfani da na&#8217;urori masu yawa, a wannan fannin a na gano cututtuka tare da taimakon radiology, Sonography, MRI, CT scan, da dai sauransu.<\/li>\r\n\t<li><strong>Psychiatry Expertise:<\/strong> Ganowa da kuma lura da psychoses da neuroses, rikicewar kwakwalwa, rikicewar bacci, da sauransu yana daya daga cikin ayyukan wannan rukunin na likitoci.<\/li>\r\n\t<li><strong>Pathology Expertise:<\/strong> Binciken tarihi na cututtuka shine aikin wannan rukuni na likitoci. Idan an cire ciwo daga jikin majinyaci a lokacin tiyata, masu ilimin cututtuka za su gaya maka ko abun da aka ce yana dauke da kansa ko a&#8217;a! Ko kuma a wane mataki na girma da mamayewa kansar ke ciki.<\/li>\r\n\t<li><strong>Ophthalmology Specialty:<\/strong> Wa\u0257annan likitocin suna bincika da magance kowasu irin cututtuka da matsaloli na ido.<\/li>\r\n\t<li><strong>Medical Genetics Specialty:<\/strong> Su na gano cututtukan gado wa\u0257anda suke yaduwa daga iyaye zuwa yara, tare da magance su. Haka kuma su na iya ba da shawarwari a kan \u0199wayoyin halitta da gwaje-gwajen tantancewa. Wa\u0257annan \u0199wararrun suna amfani da ha\u0257in gwiwar Molecular Genetics, Cytogenetics da gwaje-gwajen sinadarai don ganowa da magance cuta.<\/li>\r\n\t<li><strong>Microbiologists:<\/strong> Su kuma suna nazari ne a kan girman microorganism irin su bacteria, virus, fungi, da ala\u0199arsu da jikin \u0257an adam, su na gano dlilin rashin lafiya sannan su ayyana magani. Masana microbiology galibi su na gudanar da ayyukansu na bincike ne a laboratory domin inganta ilimin kimiyya ko masana&#8217;antar likitanci.<\/li>\r\n\t<li><strong>Optometry:<\/strong><span class=\"VIiyi\" lang=\"fa\"><span class=\"JLqJ4b ChMk0b C1N51c\" data-language-for-alternatives=\"fa\" data-language-to-translate-into=\"en\" data-phrase-index=\"0\">\u0199wararre ne da ke gudanar da gwaje-gwajen farko a fannin gani. Yana iya auna yanayin gani na majinyaci kuma ya rubuta kayan taimako don daidaita gani ko wani nau&#8217;i na kayan jinya bayan magani (motsa jiki na idanu, shawarwari, da sauransu) idan ta kama kuma ya tura majinyacin wurin likitan ido.<\/span><\/span><\/li>\r\n\t<li><strong>Parasitology Specialty:<\/strong> Su kuma wa\u0257annan mutanen su na hul\u0257a ne da \u0199wayoyin cuta (\u0199wayoyi irin bacteria, virus, tsutsa da \u0199wari) da ke rayuwa a jikin mutum. Wa\u0257annan \u0199wararrun su na amfani da hanyoyin da su ka koya daga cell biology, bioinformatics, biochemistry, molecular biology, immunology, genetics, da ecology. Haka kuma akwai wannan kwas \u0257in a Veterinary Sciences domin gano cutukan da ke jikin dabbobi.<\/li>\r\n<\/ul>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Jamioin_karatun_likitanci_a_Iran\"><\/span>Jami&#8217;o&#8217;in karatun likitanci a Iran<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>Tawagar Tolu Safiran Noor sun kawo muku jerin makarantun da ke gabatar da kwas \u0257in likitanci a ci gaban wannan rubutu. Za ku iya samun \u0199arin bayani game da manyan jami&#8217;o&#8217;in Iran da a ke karatun likitanci hakazalika ku\u0257in makarantar kowace daga cikinsu.<\/p>\r\n<ol>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/urmia-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Urmia University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/isfahan-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Isfahan University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/iran-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Iran University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/tehran-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Tehran University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/tabriz-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Tabriz University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/shahid-beheshti-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Shahid Beheshti University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/shiraz-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Shiraz University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/kurdistan-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Kurdistan University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/mazandaran-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Mazandaran University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/kerman-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Kerman University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li>Ahvaz Jondishapur University of Medical Sciences<\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/kashan-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Kashan University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/mashhad-university-of-medical-sciences\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Mashhad University of Medical Sciences<\/a><\/li>\r\n<\/ol>\r\n<hr \/>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Tambayoyin_da_a_ke_yi_game_da_karatun_likitanci_a_Iran\"><\/span>Tambayoyin da a ke yi game da karatun likitanci a Iran<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<ol>\r\n\t<li>\r\n<h4><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Daura_nawa_kwas_%C9%97in_likitanci_yake_da\"><\/span><strong>Daura nawa kwas \u0257in likitanci yake da?<\/strong><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p>Tsarin karatun likitanci na gama-gari yana da daurori guda hu\u0257u kamar haka; basic sciences, physiopathology, clinical internship, da internship.<\/p>\r\n<\/li>\r\n\t<li>\r\n<h4><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Kwas_%C9%97in_General_Medicine_da_Specialization_shekara_nawa_yake_%C9%97auka\"><\/span><strong>Kwas \u0257in General Medicine da Specialization shekara nawa yake \u0257auka?<\/strong><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p>General Medicine na \u0257aukar shekara 8 zuwa 9, specialization kuma ya danganci fannin da ake bu\u0199ata amma yana \u0257aukar a\u0199alla shekara 4.<\/p>\r\n<\/li>\r\n\t<li>\r\n<h4><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Shin_kwasa-kwasan_medicine_da_na_Allied_health_professions_%C9%97aya_ne\"><\/span><strong>Shin kwasa-kwasan medicine da na Allied health professions \u0257aya ne?<\/strong><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p>A&#8217;a, mabambantan kwasa-kwasai ne haka darusan su ma daban-daban ne.<\/p>\r\n<\/li>\r\n\t<li>\r\n<h4><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Minene_amintaccen_shafin_maaikatar_lafiya\"><\/span><strong>Minene amintaccen shafin ma&#8217;aikatar lafiya?<\/strong><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p><a href=\"https:\/\/behdasht.gov.ir\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">behdasht.gov.ir<\/a><\/p>\r\n<\/li>\r\n<\/ol>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_38998\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"38998\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>Karanta kwas \u0257in likitanci shi ne burin mafi yawan matasa masu karatu. Kwas \u0257in likitanci \u0257aya ne daga cikin kwasa-kwasai masu riba sosai wanda duk shekara yana jan hankalin \u0257alibai masu yawa zuwa gare shi. Ku kasance tare da mu&#8230;","protected":false},"author":165,"featured_media":35469,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[1056,981,972,398],"tags":[1057],"class_list":["post-38998","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fitattun-labarai","category-labarai","category-shafi","category-uncategorized-hau","tag-iran-hau"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/38998","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/users\/165"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=38998"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/38998\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/35469"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=38998"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=38998"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=38998"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}