{"id":48974,"date":"2023-11-11T13:15:50","date_gmt":"2023-11-11T09:45:50","guid":{"rendered":"https:\/\/edutsn.com\/karatu-a-petroleum-university-of-technology\/"},"modified":"2024-02-29T10:34:19","modified_gmt":"2024-02-29T07:04:19","slug":"karatu-a-petroleum-university-of-technology","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/karatu-a-petroleum-university-of-technology\/","title":{"rendered":"Karatu a Petroleum University of Technology"},"content":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_48974\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"48974\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" =0 title=\"\"><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div><p><b>Petroleum University of Technology<\/b> Jami&#8217;ar gwamnati ce wadda ta \u0199unshi kwalejin Petroleum na <a href=\"https:\/\/edutsn.com\/ahwaz\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Ahvaz<\/a>, Kwalejin Petroleum na <a href=\"https:\/\/edutsn.com\/abadan\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Abadan<\/a>, Kwalejin Petroleum na <a href=\"https:\/\/edutsn.com\/tehran\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Tehran,<\/a> da kwalejin kimiyyar teku na Mahmud Abad, wasu ne daga cikin cibiyoyin koyarwa na gaba da sakandare a Iran. Ku kasance tare da mu domin samun cikakken bayani game da karatu a jami&#8217;ar fasahar man fetur (Petroleum University of Technology).<\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Gabatarwa\"><\/span>Gabatarwa<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>Petroleum University of Technology jami&#8217;a ce ta gwamnati a garin Abadan na lardin Khozestan, wadda aka assasa a shekarar 1939. A halin yanzu akwai \u0257alibai 300 da malamai 77 a jami&#8217;ar. Jami&#8217;ar na da lambar yabo, kuma zuwa yanzu ta wallafa ma\u0199ala 2362 na ilimi a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami&#8217;ar fasahar man fetur ta mallaki lambar yabo, sannan ta wallafa mujalla 2 na musamman, kuma zuwa yanzu ta shirya taruka 7. Har ila yau, jami&#8217;ar ta yi nasarar wallafa ma\u0199ala 2013 a matakin \u0199asa da \u0199asa. A shekarar 2023, manazarta da masu bincike na jami&#8217;ar sun wallafa akasarin ma\u0199alolinsu ne da muhimman kalmomin &#8220;pushing resistance&#8221; da &#8220;Shallow wells&#8221;.<\/p>\r\n<p>A halin yanzu, jami&#8217;ar fasahar man fetur na kar\u0253ar \u0257alibai a kowace shekara a duka makarantunta 4, a mabambantan kwasa-kwasai ta hanyar jarabawar shiga ta \u0199asa. Tana kar\u0253ar \u0257alibai ne a matakin digiri, mastas, da PhD, sannan ana koyar da duka muhimman darusa (specialized courses) a yaren turanci ne. A matakin \u0199asa da \u0199asa, ana yi wa wannan jami&#8217;a la\u0199abi da sunan &#8220;PUT&#8221;.<\/p>\r\n<h2><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-39036 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/%D8%AF%D8%A7%D9%86%D8%B4%DA%AF%D8%A7%D9%87-%D8%B5%D9%86%D8%B9%D8%AA-%D9%86%D9%81%D8%AA-2.jpg\" alt=\"Karatu a Petroleum University of Technology\" width=\"700\" height=\"700\" title=\"\"><\/h2>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Martabar_Jamia\"><\/span>Martabar Jami&#8217;a<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\">Wannan jami&#8217;a ta yi nasarar tarbiyyantar da injiniyoyi da \u0199wararrun masana a fannoni daban-daban masu ala\u0199a da masana&#8217;antun man fetur, wanda hakan ya taimaka sosai wurin bun\u0199asa masana&#8217;antun man fetur a fa\u0257in duniya. Ko da yaushe ana jin nasarori da \u0199aurin suna na \u0199wararrun masan wa\u0257anda suka samu horo a wannan jami&#8217;a, a mafi yawan jami&#8217;o&#8217;i da manyan kamfanoni na duniya.<br \/>\r\nA bayyane yake cewa jajircewa da \u0199o\u0199arin da ake yi a cikin jami&#8217;ar fasahar man fetur zai da\u0257a \u0199aruwa ne a kullum, hakazalika masana&#8217;antar man fetur na da fata wurin samar da gagarumin cigaba ta hanyar \u0199wararrun masana da ma&#8217;aikatan wannan jami&#8217;ar.<\/span><\/span><\/p>\r\n<p>Bisa dogaro da sabon bayanin martabar jami&#8217;o&#8217;i da tsarin ranking na &#8220;Scimago&#8221; ya fitar a shekarar 2022, a fannin &#8220;Geology&#8221;, jami&#8217;ar fasahar man fetur ta samu matsayi na farko tsakanin jami&#8217;o&#8217;in Iran, matsayi na farko a gabas ta tsakiya, da kuma matsayi na 7 a duniya. Kamar yadda wannan tsarin raking \u0257in ya nuna, jami&#8217;ar fasahar man fetur (a mabambantan fannoni), ta sami matsayi na 697 a duniya.<\/p>\r\n<p>A tsarin ranking na C. W. U. R kuma, a shekarar 2017, jami&#8217;ar fasahar man fetur ta samu matsayi na 7 tsakanin manyan jami&#8217;o&#8217;in duniya a fannin Petroleum Engineering.<\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Makarantu\"><\/span>Makarantu<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<ul>\r\n\t<li>Abadan Faculty of Petroleum<\/li>\r\n\t<li>Ahvaz Faculty of Petroleum<\/li>\r\n\t<li>Tehran Faculty of Petroleum<\/li>\r\n\t<li>Mahmudabad Faculty of Petroleum<\/li>\r\n<\/ul>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Tehran_Faculty_of_Petroleum\"><\/span><span id=\"\u062f\u0627\u0646\u0634\u06a9\u062f\u0647_\u0646\u0641\u062a_\u062a\u0647\u0631\u0627\u0646\" class=\"mw-headline\">Tehran Faculty of Petroleum<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/tehran\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Tehran<\/a> Faculty of Petroleum ita ce makarantar Accounting da Financial sciences na masana&#8217;antar mai ta \u0199asa wadda aka assasa a shekarar 1957 inda ta fara aiki a matsayin cibiyar koyrwa da bincike domin samarwa da bun\u0199asa kimiyyar \u0257an&#8217;adam da kuma samar da bu\u0199atun masana&#8217;antun man fetur na ilimi da bincike na \u0199asa. Wannan kwalejin ita ce ta fara kwas \u0257in Accounting a Iran.<\/p>\r\n<p>Domin tarbiyyantar da ma&#8217;aikata gwargwadon yawan bu\u0199atun masana&#8217;antun mai a fannoni da matakan karatu daban-daban musamman fannin Human Science, jami&#8217;ar ta fara kar\u0253ar \u0257alibai tun daga watan September na shekarar 2013 a matakin mastas, a fannoni 4 na Oil and Gas Economics, Oil and Gas Law, Financial Management, da Management of hydrocarbon reservoirs. A shekarar 2014, an sanya kwas \u0257in Project Management a jerin kwasa-kwasan wannan kwalejin.<\/p>\r\n<p>Karon farko kenan da aka fara wa\u0257annan kwasa-kwasai uku a Iran; Management of Hydrocarbon Reservoirs, Finance, da Investment in Oil and Gas. A lokaci guda, an shirya tsarin karatu na kwas \u0257in Management of Hydrocarbon Reservoirs da na Financing and Investment in Oil and Gas ne a wannan kwalejin.<\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Ahvaz_Faculty_of_Petroleum\"><\/span><span id=\"\u062f\u0627\u0646\u0634\u06a9\u062f\u0647_\u0646\u0641\u062a_\u0627\u0647\u0648\u0627\u0632\" class=\"mw-headline\">Ahvaz Faculty of Petroleum<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>Ayyukan koyarwa na <a href=\"https:\/\/edutsn.com\/ahwaz\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Ahvaz<\/a> Faculty of Petroleum sun fara ne daga shekarar 1983 (a lokacin ya\u0199in Iran da Iraq). An gudanar da wa\u0257annan ayyukan ilimi da na bincike ne a fannin tace mai da iskar gas, da kuma Petrochemical Engineering.<\/p>\r\n<p>Wannan kwaleji ita ce mafi girma daga cikin kwalejojin jami&#8217;ar, Kuma tana cikin garin Ahvaz. Kwas mafi muhimmanci a matakin digiri na wannan kwalejin shi ne Petroleum Engineering, sannan akwai kwasa-kwasan Electrical da Chemical Engineering.<\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Abadan_Faculty_of_Petroleum\"><\/span><span id=\"\u062f\u0627\u0646\u0634\u06a9\u062f\u0647_\u0646\u0641\u062a_\u0622\u0628\u0627\u062f\u0627\u0646\" class=\"mw-headline\">Abadan Faculty of Petroleum<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>Kafin mai ya dawo \u0199ar\u0199ashin ikon gwamnati, kamfanin mai na Birtaniya da Iran yana da makaranta a Abadan wadda ke kar\u0253ar \u0257alibai wa\u0257anda suka kammala karatun sakandare tare da ba su digirin Engineering bayan shekaru uku na karatu. Kashi biyu bisa uku na injiniyoyin kasar Iran na masana&#8217;antun mai wannan cibiyar ce ta samar da su, sauran kuma an samar da su ne daga babban gidan ajiye kayan tarihi da ke birnin Tehran.<\/p>\r\n<p>Bayan mayar da man fetur \u0199ar\u0199ashin gwamnati da kuma cire hannu daga kamfanin mai na Iran da Birtaniya, an rufe wannan makarantar mai. Bayan juyin mulkin 28 Mordad a shekarar 1953, Ali Asgar Pourhomayoun ya yanke shawarar kafa kwalejin man fetur a makarantar fasaha ta gaba da sakandare, wanda aka ware daga majalisar al\u2019adu aka mayar da ita zuwa majalisar tattalin arziki ta \u0199asa shekaru biyar kafin lokacin. Ministan tattalin arziki na \u0199asa Fakhreddin Shadman wanda ya hau kan karagar mulki a shekara ta gaba, yana da ra&#8217;ayin cewa ya kamata \u0257aliban jami&#8217;ar man fetur su karanci darussan theory a Tehran, darussan practical kuma a Abadan, amma ra&#8217;ayin Reza Jafari ministan harkokin man fetur da al&#8217;adu shi ne a mayar da malamai Abadan, inda aka aiwatar da wannan ra&#8217;ayin nasa bisa amincewar majalisa. <sup id=\"cite_ref-:1_6-1\" class=\"reference\"><\/sup><\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Mahmodabad_Faculty_of_Marine_Science\"><\/span><b>Mahmodabad Faculty of Marine Science<\/b><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>\u018aaya ce daga cikin cibiyoyin koyar da marine sciences na farko da suka fara aiki a shekara ta 1985 a birnin Mahmudabad da lardin Mazandaran. Wannan cibiya, wacce \u0257aya ce daga cikin kwalejojin jami&#8217;ar fasahar man fetur, tana horar da ma&#8217;aikatan ruwa da za su yi aiki a kan jiragen ruwa da ke tafiya tekuna. Bayan kammala karatun \u0257alibai a wannan cibiya, yawanci kamfanonin sufurin jiragen ruwa na \u0199asar Iran ne ke \u0257aukarsu aiki, kamar kamfanin dakon man fetur na Iran da kuma jigilar kayayyaki na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.<\/p>\r\n<h2><img decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-39024 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/%D8%AF%D8%A7%D9%86%D8%B4%DA%AF%D8%A7%D9%87-%D8%B5%D9%86%D8%B9%D8%AA-%D9%86%D9%81%D8%AA-3.jpg\" alt=\"Karatu a Petroleum University of Technology\" width=\"700\" height=\"700\" title=\"\"><\/h2>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Kwasa-Kwasai\"><\/span>Kwasa-Kwasai<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p><strong>Digiri:<\/strong><\/p>\r\n<ul>\r\n\t<li>\r\n<div>Safety Engineering and Technical Inspection<\/div>\r\n<\/li>\r\n\t<li>Chemical Engineering<\/li>\r\n\t<li>Petroleum Engineering<\/li>\r\n\t<li>Mechanical Engineering<\/li>\r\n\t<li>Electrical Engineering<\/li>\r\n\t<li>Acoounting<\/li>\r\n<\/ul>\r\n<p><strong>Masters:<\/strong><\/p>\r\n<ul>\r\n\t<li>Chemical Engineering &#8211; HSE<\/li>\r\n\t<li>Oil Exploration Engineering<\/li>\r\n\t<li>Mechanical Engineering &#8211; applied design<\/li>\r\n\t<li>Civil Engineering &#8211; Engineering of coasts, ports and marine structures<\/li>\r\n\t<li>Technical Inspection Engineering<\/li>\r\n\t<li>Petroleum Engineering &#8211; Exploitation<\/li>\r\n\t<li>Petroleum Engineering &#8211; hydrocarbon tanks<\/li>\r\n\t<li>Petroleum Engineering &#8211; drilling<\/li>\r\n\t<li>Gas Processing and Transmission Engineering<\/li>\r\n\t<li>Instrumentation and Automation Engineering<\/li>\r\n\t<li>Finance &#8211; financing and investing in oil and gas<\/li>\r\n\t<li>Oil and Gas Law<\/li>\r\n\t<li>Oil and gas Economics<\/li>\r\n\t<li>Management of Hydrocarbon Reservoirs<\/li>\r\n<\/ul>\r\n<p><strong>PhD:<\/strong><\/p>\r\n<ul>\r\n\t<li>Petroleum Engineering<\/li>\r\n\t<li>Chemical Engineering &#8211; transfer phenomena and separation processes<\/li>\r\n<\/ul>\r\n<h2 align=\"justify\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Ku%C9%97in_makarantar_jamiar_fasahar_man_fetur\"><\/span>Ku\u0257in makarantar jami&#8217;ar fasahar man fetur<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<div id=\"footable_parent_47530\"\n         class=\" footable_parent ninja_table_wrapper loading_ninja_table wp_table_data_press_parent semantic_ui colored_table\">\n                <table data-ninja_table_instance=\"ninja_table_instance_0\" data-footable_id=\"47530\" data-filter-delay=\"1000\" aria-label=\"\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647 \u0648\u0632\u0627\u0631\u062a \u0639\u0644\u0648\u0645 \u0635\u0646\u0639\u062a \u0646\u0641\u062a\"            id=\"footable_47530\"\n           data-unique_identifier=\"ninja_table_unique_id_1766893348_47530\"\n           class=\" foo-table ninja_footable foo_table_47530 ninja_table_unique_id_1766893348_47530 ui table  grey nt_type_legacy_table fixed celled striped compact vertical_centered inverted footable-paging-right ninja_table_search_disabled ninja_table_pro\">\n                <colgroup>\n                            <col class=\"ninja_column_0 \">\n                            <col class=\"ninja_column_1 \">\n                    <\/colgroup>\n        <thead>\n<tr class=\"footable-header\">\n                                        <th scope=\"col\"  class=\"ninja_column_0 ninja_clmn_nm_majors \">Majors<\/th><th scope=\"col\"  class=\"ninja_column_1 ninja_clmn_nm_annualtuitionindollars \">Annual tuition in dollars<\/th><\/tr>\n<\/thead>\n<tbody>\n\n<\/tbody><!--ninja_tobody_rendering_done-->\n    <\/table>\n    \n    \n    \n<\/div>\n\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Alfanun_karatu_a_jamiar_fasahar_man_fetur\"><\/span>Alfanun karatu a jami&#8217;ar fasahar man fetur<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p align=\"justify\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\">&#8211; Domin inganta yawa da ingancin malamai da membobin tsangayar ilimi da samun sabbin fasahohi, Jami&#8217;ar fasahar man fetur tana da damar yin ayyuka na ha\u0257in gwiwa tare da sauran manyan cibiyoyin bincike da masana&#8217;antu na duniya.<\/span><\/span><\/p>\r\n<p align=\"justify\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\">&#8211; Jami&#8217;ar na ba wa \u0257alibanta damar yin amfani da wuraren da suka dace na karatu da walwala a yayin karatunsu.<br \/>\r\n-Saboda kusancin da take da shi da \u0199ungiyoyin mai da iskar gas na musamman, jami&#8217;o&#8217;i da manyan kamfanonin mai na duniya, jami&#8217;ar ta samar wa da \u0257alibai da malamanta damar aiki tare da wa\u0257annan \u0199ungiyoyin.<\/span><\/span><\/p>\r\n<p align=\"justify\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\">&#8211; A tsawon lokacin karatunsu, \u0257aliban wannan jami&#8217;a suna da damar kasancewa a cikin masana&#8217;antar man fetur da kuma yiwuwar samun gogewar ilimin kimiyya a masana&#8217;antar.<\/span><\/span><\/p>\r\n<p align=\"justify\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\">&#8211; Gabatar da abubuwan karatu a harshen turanci yana \u0257aya daga cikin alfanun karatu a wannan jami&#8217;a.<\/span><\/span><\/p>\r\n<p align=\"justify\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\">&#8211; Wurare na musamman na ilimi da jin da\u0257in rayuwa wa\u0257anda ke taimaka wa \u0257alibai wurin samun ingantaccen ilimi a wannan jami&#8217;a.<\/span><\/span><\/p>\r\n<p align=\"justify\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\"><span class=\"RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver RadEDomMouseOver\">&#8211; Ba da tallafin karatu ga \u0257alibai.<\/span><\/span><\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Ababen_More_Rayuwa\"><\/span>Ababen More Rayuwa<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<ul>\r\n\t<li>Ala\u0199a da muhimman ma&#8217;adanan bayanai da ingantattun wallafe-wallafen ilimi na \u0199asashen waje kamar Onepetro, tare da damar downloading kyauta<\/li>\r\n\t<li>Zuwan manyan kamfanonin mai irin su Total France don gudanar da hirarraki da \u0257aliban da suka kammala karatunsu tare da bayar da scholarship<\/li>\r\n\t<li>Intanet mai yawa da cajin kai-tsaye na mako-mako, ba tare da biyan ku\u0257i ba<\/li>\r\n\t<li>Gidan cin abinci mai inganci, mai sayar da abinci sau uku a kowace rana<\/li>\r\n\t<li>Kar\u0253ar litattafai da takardu kyauta wa\u0257anda malamai suka yi amfani da su wurin koyar da \u0257alibai a kowane zangon karatu a kwalejin<\/li>\r\n\t<li>Kar\u0253ar tallafin karatu a kowane wata<\/li>\r\n\t<li>Cikakkun kayan wasanni da na more rayuwa (filin \u0199wallo, swimming pool, gym, zauren wasannin badminton, dart, chess, da sauransu) a kusa da hostel<\/li>\r\n\t<li>Amfani da mafi ingancin kayan aikin \u0257akunan gwaje-gwaje idan an kwatanta da sauran jami&#8217;o&#8217;in kasar<\/li>\r\n<\/ul>\r\n<h2><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-39028 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/%D8%AF%D8%A7%D9%86%D8%B4%DA%AF%D8%A7%D9%87-%D8%B5%D9%86%D8%B9%D8%AA-%D9%86%D9%81%D8%AA-4.jpg\" alt=\"Karatu a Petroleum University of Technology\" width=\"700\" height=\"700\" title=\"\"><\/h2>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Wuraren_kwanan_%C9%97alibai\"><\/span>Wuraren kwanan \u0257alibai<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Wurin_kwanan_kwalejin_Abadan\"><\/span><span style=\"font-size: 16px;\"> Wurin kwanan kwalejin Abadan:<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p><span style=\"font-size: 16px;\">Wannan kwalejin na da gine-gine guda 7 masu hawa biyu-biyu, kowane hawa na da sassa daban-daban masu \u0257akunan kwanan mutum 4, mutum 3, da na mutum 2 tare da ban\u0257akai, talabijin, kitchen, firiji, ac, teburin karatu da sauran kayan bu\u0199atar \u0257alibai.<br \/>\r\nWannan hostel zai iya \u0257aukar kimanin mutum 650.<\/span><\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Wurin_kwanan_kwalejin_Tehran\"><\/span><span style=\"font-size: 16px;\"> Wurin kwanan kwalejin Tehran:<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p><span style=\"font-size: 16px;\">A wannan kwalejin ana ba duka \u0257aliban da suke nesa masu bu\u0199ata wurin kwana. Ma&#8217;aikatar ilimi ta tantance duka wuraren kwanan wannan kwalejin sannan ana bai wa \u0257alibai masauki ne bisa la&#8217;akari da tsawon lokacin karatunsu. Kwalejin na da hostel guda biyu.<\/span><\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Hostel_%C9%97in_kwalejin_Marine_Sciences_na_Mahmodabad\"><\/span><span style=\"font-size: 16px;\"> Hostel \u0257in kwalejin Marine Sciences na Mahmodabad:<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p><span style=\"font-size: 16px;\">Saboda gabatar da kwasa-kwasai da ake karantawa dare da rana, jami&#8217;ar ta yi \u0199o\u0199arin samar da wuraren kwanan \u0257alibai masu yalwa tare da abubuwan bu\u0199ata da suka dace. Kwalejin na da wuraren kwana kusan guda 50 masu \u0257akunan kwanan mutum 2 \u0257auke da abubuwan bu\u0199atun \u0257alibai kamar gado, teburi, kujeru, na&#8217;urorin \u0257umamawa da sanyaya wuri, da sauransu. Hakazalika akwai \u0257akin malamai \u0257auke da isassun kayan aiki da aka tanada domin malamai. <\/span><\/p>\r\n<p><span style=\"font-size: 16px;\">Bugu da \u0199ari, akwai yanayi mai da\u0257i a inda wuraren kwanan suke tare da sautin ka\u0257awar taguwar ruwa wanda ke \u0199ara samar wa \u0257alibai sukuni.<br \/>\r\nHakazalika kwalejin na ba ma \u0257alibai abinci sau uku a rana (safe, rana da dare) a duka ranakun sati (har a ranakun hutu), da tunanin cewa abincin da ake ba \u0257alibai ya cika dukan sharu\u0257a ta fuskar yawa da kuma ingancinsa.<\/span><\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Yanayin_wurin_da_jamiar_take\"><\/span>Yanayin wurin da jami&#8217;ar take<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p><strong>Adireshi:<\/strong><\/p>\r\n<p>Tehran: Titin Sattarkhan, titin Shahid Sadeghipour na kudu, titin Ghasemizadeyan<\/p>\r\n<p>Ahvaz: Kot Abdallah, Kot, babban titin Behbahani<\/p>\r\n<p>Abadan: <span dir=\"rtl\">Bawardeh ta yamma, Kwalejin man fetur na Abadan<\/span><\/p>\r\n<p>Mahmodabad: Mahmodabad, Sadaf, titin Nateqnori<\/p>\r\n<p><strong>Shafin Jami&#8217;a:<\/strong><a href=\"https:\/\/www.put.ac.ir\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">https:\/\/www.put.ac.ir<\/a><\/p>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_48974\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"48974\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>Petroleum University of Technology Jami&#8217;ar gwamnati ce wadda ta \u0199unshi kwalejin Petroleum na Ahvaz, Kwalejin Petroleum na Abadan, Kwalejin Petroleum na Tehran, da kwalejin kimiyyar teku na Mahmud Abad, wasu ne daga cikin cibiyoyin koyarwa na gaba da sakandare a&#8230;","protected":false},"author":127,"featured_media":39035,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[973,974,972],"tags":[975],"class_list":["post-48974","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-makarantu","category-makarantun-da-ke-arashin-maaikatar-ilimi","category-shafi","tag-khozestan"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/48974","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/users\/127"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=48974"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/48974\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/39035"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=48974"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=48974"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=48974"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}