{"id":50473,"date":"2023-11-15T12:31:55","date_gmt":"2023-11-15T09:01:55","guid":{"rendered":"https:\/\/edutsn.com\/karatu-a-garin-arak\/"},"modified":"2024-05-16T13:17:07","modified_gmt":"2024-05-16T09:47:07","slug":"karatu-a-garin-arak","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/karatu-a-garin-arak\/","title":{"rendered":"Karatu a garin Arak"},"content":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_50473\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"50473\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" =0 title=\"\"><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div><p>Garin <b>Arak<\/b> \u0257aya ne daga cikin manyan garuruwan \u0199asar Iran kuma \u0257aya daga cikin garuruwa mafi girma na tsakiyar \u0199asar. Garin Arak ne babban birnin lardin Markazi. A kowace shekara tawagarmu na cin karo da adadi mai yawa na \u0257alibai masu sha&#8217;awar karatu a garin Arak. A cigaban rubutumu za mu kawo muku bayanai dangane da wannan gari.<\/p>\n<h2><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-39613 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/%D8%AA%D8%AD%D8%B5%DB%8C%D9%84-%D8%AF%D8%B1-%D8%A7%D8%B1%DA%A9-1.jpg\" alt=\"Karatu a garin Arak\" width=\"700\" height=\"707\" title=\"\"><\/h2>\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Arak\"><\/span>Arak<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\n<p>Ta kudu, garin Arak na kewaye da tsaunukan Sefidkhani, tsaunukan Nazm Abad, tsaunin Sorkh Koh (Kuhe Sorkh), ta yamma kuma akwai tsaunin Mud a zagaye da garin. Duwatsun da ke kewaye da garin sun ha\u0257a da duwatsun markazi da wani \u0253angare na duwatsun Zagros.<\/p>\n<p>Kogin Qarekhirz (wanda aka fi sani da busasshen kogi) shi ne kawai kogin da ya ratsa ta cikin garin. Wannan kogin idonsa yana duwatsun Qarekhriz, bayan ya ji\u0199a \u0199asashen da ke kusa da garin, ya yanko ta yammacin garin sannan ya gangara zuwa cikin tafkin Mighan. Kogin yana \u0199afewa a lokacin rani. Daga cikin matsalolin da kogin ke fuskanta akwai shigowar najasa daga wasu sassan garin zuwa cikinsa da kuma gur\u0253atar ruwa.<\/p>\n<p>Akwai koren sarari mai yawa a garin Arak ta yadda kowane mutum zai samu murabba&#8217;in mita 22.57 na koren fili, irin wannan \u0199iyasin da aka yi na gaba\u0257ayan \u0199asar kowane mutum a Iran zai samu murabba&#8217;in mita 7.5 na koren fili. Duk da dai yanzu akwai matsalar rashin isasshen ruwa wanda hakan ya haifar wa da wa\u0257annan koren wuraren matsala har ya zama wasunsu sun bushe.<\/p>\n<p>Akwai koren filaye da za su kai kusan hekta 300 bayan wadanda aka samar cikin gari wanda su kuma a jimilla girmansu zai kai kusan hekta 100 wa\u0257anda ake ba ruwa ta hanyar rijiyoyin ruwan da ba na sha ba, da magudanan ruwa na cikin gari. Hakazalika ta yammacin garin akwai koren sarari na Senejan da na Korehrud. Girman duka koren filayen na cikin garin Arak ya kai hekta 1,336 wanda daga ciki akwai lambuna 125. Mafi yawan koren sararin Arak nau&#8217;in lambu ne a yankunan Sanjan da Korerood.<\/p>\n<h2><img decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-39617 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/%D8%AA%D8%AD%D8%B5%DB%8C%D9%84-%D8%AF%D8%B1-%D8%A7%D8%B1%DA%A9-2.jpg\" alt=\"Karatu a Arak\" width=\"700\" height=\"707\" title=\"\"><\/h2>\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Zirga-Zirga\"><\/span>Zirga-Zirga<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\n<p>Garin Arak na da filin jirgi na \u0199asa da \u0199asa guda \u0257aya wanda yana daga cikin filayen jirage na farko-farko a \u0199asar Iran. Ba mu san takamaimiyar shekarar da aka gina filin jirgin ba amma dai a hukumance an fa\u0257a\u0257a shi a shekarar 1938, kodayake an kawo jirage a ciki tun kafin wannan lokacin. Har zuwa kafin fara aiwatar da aikin \u0199ara yawan hanyar jirgi, jiragen cikin gida ne kawai suke amfani da filin jirgin tare da jiragen sojoji, sai matsakaitan jirage da jiragen \u0257aukar kaya. Manyan jirage ba za su iya sauka a filin jirgin ba.<\/p>\n<p>A shekarar 2013 ne bayan aiwatar da tsarin fa\u0257a\u0257a filin jirgin sama na Arak a \u0253angarorin tashin jirage da hanyarsu, sannan ne aka samu yiwuwar saukar manyan jirage har da jirage nau&#8217;in &#8216;airbus&#8217; a filin jirgin. Yanzu haka a filin jirgin Arak akwai jirage masu zuwa garuruwan Tehran, Mashhad, da Asaluyeh a kowane sati.<\/p>\n<p>An jima da jonawa garin na Arak layin jirgin \u0199asa, garin na kan layin jirgin \u0199asa na arewa zuwa kudancin \u0199asar Iran. Layin jirgin \u0199asa ya taka muhimmiyar rawa wajen cigaban garin ta kowane \u0253angare. Yankin da aka ware a \u0199ar\u0199ashin kulawar tashar jirgin \u0199asa ta garin Arak ya fara ne daga tashar Saghe wadda yanki ce a cikin lardin Qom, har zuwa tashar Mumin Abad ta lardin Lorestan ta wani \u0253abgaren kuma har zuwa tashar Kermanshah, kodayake ana dab da samarwa lardin Kermanshah da tashar jirgin \u0199asa daban.<\/p>\n<p>Garin Arak na da tashar mota guda uku:<\/p>\n<ul>\n\t<li>Tashar Payane Markazi: Wadda ke daura da hotel \u0257in Amirkabir mai tauraro 5.<\/li>\n\t<li>Tashar Payane Farahan: A arewacin garin Arak daura da randabawul na Amirkabir.<\/li>\n\t<li>Tashar Payane Ghadir: A kudu maso yammacin garin na Arak daura da Meidane Basij.<\/li>\n<\/ul>\n<p>An assasa sashen motocin bus na gari a shekarar 1991 kuma tana da layi daban-daban na motocin bus masu yawo cikin gari da unguwannin bayan gari. A shekarar 2013 motocin bus 166 ne su ka yi aikin jigilar mutane a layuka 45. Mota 64 daga ciki da gas suke aiki, sauran 102 kuma da man disel suke aiki. A watanni uku na farkon shekarar 2013, motocin sun yi jigilar kimanin mutane 13,300,059 zuwa wurare daban-daban na cikin garin Arak. Har ila yau an hannunta kula da duka layukan bus zuwa sashe na musamman a ma&#8217;aikatar tu\u0199in bus ta <a href=\"https:\/\/arak.ir\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">garin Arak.<\/a><\/p>\n<h2><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-39609 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/%D8%AA%D8%AD%D8%B5%DB%8C%D9%84-%D8%AF%D8%B1-%D8%A7%D8%B1%DA%A9-4.jpg\" alt=\"Karatu a Arak\" width=\"700\" height=\"700\" title=\"\"><\/h2>\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Wuraren_sha%C6%99atawa\"><\/span>Wuraren sha\u0199atawa<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Park\"><\/span><span id=\"\u067e\u0627\u0631\u06a9\u200c\u0647\u0627\" class=\"mw-headline\">Park<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\n<p>Daga cikin wuraren sha\u0199atawa na garin Arak akwai:<\/p>\n<ul>\n\t<li>Amusement Park (Laleh Park)<\/li>\n\t<li>Tufan Collection<\/li>\n\t<li>Pamchal Amusement Park<\/li>\n<\/ul>\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Cibiyoyin_kasuwanci\"><\/span><span id=\"\u0645\u0631\u0627\u06a9\u0632_\u062e\u0631\u06cc\u062f\" class=\"mw-headline\">Cibiyoyin kasuwanci<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\n<h4><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Cibiyoyin_sayayya_na_gargajiya\"><\/span><span id=\".D9.85.D8.B1.D8.A7.DA.A9.D8.B2_.D8.AE.D8.B1.DB.8C.D8.AF_.D8.B3.D9.86.D8.AA.DB.8C\"><\/span><span id=\"\u0645\u0631\u0627\u06a9\u0632_\u062e\u0631\u06cc\u062f_\u0633\u0646\u062a\u06cc\" class=\"mw-headline\">Cibiyoyin sayayya na gargajiya<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\n<p>Kasuwar garin (kasuwar Saham Sultan) baya ga salon gini na tarihi irin nata, wuri ne da mutane ke gudanar da harkokin kasuwanci na yau da kullum, bayan ta yi nasarar ajiye matsayinta na tarihi.<\/p>\n<h4><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Sabbin_cibiyoyin_kasuwanci\"><\/span><span id=\".D9.85.D8.B1.D8.A7.DA.A9.D8.B2_.D8.AE.D8.B1.DB.8C.D8.AF_.D9.86.D9.88.DB.8C.D9.86\"><\/span><span id=\"\u0645\u0631\u0627\u06a9\u0632_\u062e\u0631\u06cc\u062f_\u0646\u0648\u06cc\u0646\" class=\"mw-headline\">Sabbin cibiyoyin kasuwanci<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\n<p>Baya ga tsofaffin cibiyoyin kasuwanci na tarihi akwai na zamani da aka gina a shekarun bayabayannan a garin Arak, daga cikinsu akwai Golestan Shopping Complex, Asman Commercial Complex, Asman Shopping Complex, Pasaj Didar, Pasaj Sadaf, Pasaj Tala, Pasaj Tehrani, Pasaj Sana, da Pasaj Khatam.<\/p>\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Abubuwan_Tarihi\"><\/span><span id=\"\u0622\u062b\u0627\u0631_\u062a\u0627\u0631\u06cc\u062e\u06cc\" class=\"mw-headline\">Abubuwan Tarihi<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\n<ul>\n\t<li>Kasuwar Arak<\/li>\n\t<li>Makarantar Sepahdari<\/li>\n\t<li>Gidan wanka na Chaharfasl<\/li>\n\t<li>Gidan Hassanpour<\/li>\n\t<li>Ghal&#8217;e Hajvakil<\/li>\n\t<li>Karvansarae Shah Abbasi<\/li>\n<\/ul>\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Wuraren_kallo_na_%C9%97abia\"><\/span><span id=\"\u062c\u0627\u0630\u0628\u0647\u200c\u0647\u0627\u06cc_\u0637\u0628\u06cc\u0639\u06cc\" class=\"mw-headline\">Wuraren kallo na \u0257abi&#8217;a<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\n<ul>\n\t<li>Tafkin Mighan<\/li>\n\t<li>Darre Gerdo<\/li>\n\t<li>Takht Sadat<\/li>\n\t<li>Sorkh Kuh (dutsen surkhe)<\/li>\n<\/ul>\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Wuraren_addini\"><\/span><span id=\"\u062c\u0627\u0630\u0628\u0647\u200c\u0647\u0627\u06cc_\u0645\u0630\u0647\u0628\u06cc\" class=\"mw-headline\">Wuraren addini<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\n<p>Imamzadeh Muhammad Abid (zamanin safavieh), Imamzadeh Abdullah da Aminekhatoun, ma\u0199abartar Agha Nuruddeen Iraqi, tsohuwar ma\u0199abartar Arak, duk wa\u0257annan suna cikin wuraren addini na garin.<\/p>\n<p>Cocin Masrup Moghaddas \u0257aya ce daga cikin cocuna biyu na garin Arak wadda aka ginata a zamanin daular Qajar. Sai hubbaren da aka gina a \u0199auyen Morad Abad a lokacin daular Saljoughi.<\/p>\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Gidajen_tarihi\"><\/span><span id=\"\u0645\u0648\u0632\u0647\u200c\u0647\u0627\" class=\"mw-headline\">Gidajen tarihi<\/span><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\n<p>Daga cikin gidajen tarihin garin Arak awai gidan tarihi na Chaharfasl, na Mufakher, Sultan Abad, gidan tarihi na Anthropology, gidan tarihi na sana&#8217;o&#8217;in hannu, gidan tarihi na Biodiversity, gidan tarihi na duwatsu da ma&#8217;adanai, da kuma gidan tarihi na Amozesh Parvaresh. Hakazalika ana kan gina babban gidan tarihi na garin Arak da gidan tarini na Defa Moghaddas yanzu haka.<\/p>\n<h2><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-39605 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/%D8%AA%D8%AD%D8%B5%DB%8C%D9%84-%D8%AF%D8%B1-%D8%A7%D8%B1%DA%A9-3.jpg\" alt=\"Karatu a Arak\" width=\"700\" height=\"700\" title=\"\"><\/h2>\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Ingantattun_jamioi\"><\/span>Ingantattun jami&#8217;o&#8217;i<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\n<ul>\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/arak-university\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Jami&#8217;ar Arak (University of Arak)<\/a><\/li>\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/arak-university-of-medical-sciences\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Arak University of Medical Sciences<\/a><\/li>\n<\/ul>\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Karatu_a_Arak\"><\/span>Karatu a Arak<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\n<p>Karatu a garin Arak na da fa&#8217;idoji masu yawa ga \u0257alibai. Fa&#8217;idoji kamar sau\u0199in farashin rayuwa, karatu a amintattun jami&#8217;o&#8217;i irin su Arak University of Medical Scienes da University of Arak.<\/p>\n<p>Akwai cibiyoyin jami&#8217;o&#8217;i da cibiyoyin ilimi guda 38 a lardin Markazi. Jami&#8217;o&#8217;in wannan lardin sun ke\u0253antu da wallafa mujallolin kimiyya na musamman guda 30, zuwa yanzu sun wallafa jimillar mujallu 253. Lardin Markazi ya kar\u0253i ba\u0199uncin tarukan kimiyya 50 zuwa yanzu. Hakazalika researchers na jami&#8217;o&#8217;in lardin sun wallafa ma\u0199alolin ilimi guda 39631 wanda guda 7356 daga ciki na mujalla ne, 22397 kuma na tarukan cikin gida, 7356 kuma na \u0199asa da \u0199asa. A shekarar 2018 an samu jimillar \u0257alibai 47,508 masu karatu a cikin jami&#8217;o&#8217;in lardin tare da malamai da ma&#8217;aikatan tsangayar ilimi 2,128.<\/p>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_50473\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"50473\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>Garin Arak \u0257aya ne daga cikin manyan garuruwan \u0199asar Iran kuma \u0257aya daga cikin garuruwa mafi girma na tsakiyar \u0199asar. Garin Arak ne babban birnin lardin Markazi. A kowace shekara tawagarmu na cin karo da adadi mai yawa na \u0257alibai&#8230;","protected":false},"author":127,"featured_media":39872,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[977,972],"tags":[1018],"class_list":["post-50473","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-garuruwa","category-shafi","tag-markazi-hau"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/50473","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/users\/127"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=50473"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/50473\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/39872"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=50473"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=50473"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=50473"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}