{"id":51262,"date":"2024-01-01T09:24:29","date_gmt":"2024-01-01T05:54:29","guid":{"rendered":"https:\/\/edutsn.com\/minene-biza-kuma-minene-fasfo\/"},"modified":"2024-12-19T17:09:56","modified_gmt":"2024-12-19T13:39:56","slug":"minene-biza-kuma-minene-fasfo","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/minene-biza-kuma-minene-fasfo\/","title":{"rendered":"Minene biza da fasfo?"},"content":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_51262\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"51262\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" =0 title=\"\"><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div><p style=\"text-align: justify;\">Idan kuna bu\u0199atar amsoshin tambayoyi kamar; minene biza da fasfo, minene bambancin biza da fasfo, kashe-kashen biza, kashe-kashen fasfo, ku kasance tare da mu. A halin yanzu, sabbin bayanan \u0199ididdiga na nuna cewa akwai \u0199asashe 195 mabambanta a doron duniya a nahiyoyi 7 na Africa, Asia, Australia, Europe, North America, South America, da Antarctica.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Kowace daga cikin \u0199asashennan 195 na da ayyanannar iyaka a \u0199asa, ruwa, ko iska kuma tana da dokokinta na musamman da suka shafi yin tafiya ko hijira. Da gaske ne dukan mu ahalin wannan duniyar ne, amma ba za mu iya sauya muhallinmu daga wata \u0199asa zuwa wata haka kawai ba tare da wani tsari ko mallakar wasu takardu na shaida ba. Hatta zama a wata \u0199asar na gajeren lokaci ba tare da takardun shaida ko wani tsari ba ba abu ne mai yiwuwa ba.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Saboda haka ku kasance tare da mu a wannan rubutun domin mu yi muku cikakken bayani akan <strong>minene biza<\/strong>, <strong>yaya ake kar\u0253ar biza<\/strong>, <strong>bambancin da ke tsakanin biza da fasfo,<\/strong> da kuma <strong>kashe-kashen biza<\/strong> tare da sauran muhimman bayanan da ya kamata ku sani game da su.<\/p>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-47295 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/visa2.jpg\" alt=\"biza da fasfo\" width=\"700\" height=\"394\" title=\"\" srcset=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/visa2.jpg 700w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/visa2-300x169.jpg 300w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/visa2-24x14.jpg 24w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/visa2-36x20.jpg 36w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/visa2-48x27.jpg 48w\" sizes=\"(max-width: 700px) 100vw, 700px\" \/><\/h2>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Minene_Biza\"><\/span>Minene Biza?<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Babu shakka da yawanku za su iya sanin me ake nufi idan an ambaci sunan biza, to amma ga wa\u0257anda ba su riga sun san ma&#8217;anar biza ba sai mu ce; biza na nufin izinin shigar mutum wata \u0199asa da ba \u0199asarsu ba.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">A ta\u0199aice za a iya cewa biza wani izini ne mai \u0257auke da sharu\u0257a da ake bayarwa idan mutum zai shiga \u0199asar da ba tasa ba na tsawon wani ayyanannen lokaci. Gwamnatin kowace \u0199asa ita ke da alhakin sanya sharu\u0257an biza ga \u01b4an wata \u0199asa da ba \u0199asarta ba ko ta \u0257aga \u0199afa ga wasu bisa la&#8217;akari da irin siyasa da al&#8217;adunta.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Biza na iya zama ta <strong>gajeren zango<\/strong> (kwana 1 har zuwa watanni) ko kuma ta dogon <strong>zango<\/strong>, sannan tana aiki ne kawai a \u0199asashen da aka bugata dominsu. Ana iya buga biza a matsayin <strong>stika<\/strong> a jikin shafukan fasfo ko kuma ta zama <strong>electronic<\/strong> wato ta cikin na&#8217;ura wadda ake bugawa <strong>online<\/strong>.<\/p>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Minene_bambancin_biza_da_fasfo\"><\/span>Minene bambancin biza da fasfo?<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Biza izinin shiga wata \u0199asa ne wadda \u0199asa ke ba mutanen da suka cika sharu\u0257an da ta gindaya na shiga \u0199asarta. Amma international passport wato fasfo takardar shaida ce (kamar dai ID card) wanda ake amfani da shi wajen gane mutanen wata \u0199asa idan sun fita wajen \u0199asarsu. Duk \u0257an \u0199asa na da fasfo na kansa kuma zai iya amfani da shi wajen neman biza ta mabambantan \u0199asashe.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Amma idan ana magana a kan bambancin da ke tsakanin biza da fasfo, za a iya cewa biza na amfani ne kawai idan akwai fasfo kuma bai yi expiring ba. Mutum zai iya neman bizar daban-daban kamar bizar yawon bu\u0257e ido ko bizar neman aiki a \u0199asar Germany ko Australia ko wata \u0199asar matsawar yana da fasfo. Wani abun dubawa a bambancin tsakanin biyunnan shi ne inganci da tasiri. Ma&#8217;anar inganci da tasiri a nan shi ne abubuwa biyunnan suna da janibobi daban-daban wanda da yawan mutane basu sani ba.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Misali idan mutum na da fasfo \u0257in \u0199asar America, baya ga yawan shekarun da fasfo \u0257in yake yi kafin ya \u0199are, yana da tasiri sosai ta yadda mutum zai iya amfani da shi wajen shiga \u0199asashe 184 ba tare da biza ba.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Amma a babin biza, tana aiki ne iya na lokacin da aka ayyana ne kawai sannan dole a duba yiwuwar shiga \u0199asa fiye da \u0257aya da ita. Misali ana iya amfani da bizar Schengen a \u0199asashe 26, hakan na nuna irin \u0199arfin tasirin wannan biza.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\"><img decoding=\"async\" class=\"size-full wp-image-47289 aligncenter\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/%D9%88%DB%8C%D8%B2%D8%A7.jpg\" alt=\"Minene biza\" width=\"700\" height=\"394\" title=\"\"><\/p>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Nauoin_Biza\"><\/span><strong>Nau&#8217;o&#8217;in Biza<\/strong><span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Yanzu kun san ma&#8217;anar biza, sai kuma bayani game da nau&#8217;o&#8217;in biza. Wannan batu ya \u0199unshi \u0253angarori daban-daban. \u0181angare mafi muhimmanci shi ne tsawon lokacin amfani da biza wanda ya kasu kashi biyu kamar haka:<\/p>\r\n<ul style=\"text-align: justify;\">\r\n\t<li><strong>Bizar gajeren zango<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Bizar dogon zango<\/strong><\/li>\r\n<\/ul>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Yana da kyau ku san cewa bayanan da suka ta&#8217;alla\u0199a da biza na da muhimmancin gaske wa\u0257anda sun zarce tunaninku sannan ko wace \u0199asa na da nata kalar dokokin da sun ke\u0253anceta ne ita ka\u0257ai. Dukda haka za mu yi \u0199o\u0199arin yi muku bayanin abunda ya sauwa\u0199a.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Da yawan mutane idan sun ji an ambaci bizar gajeren zango za su fara tunanin bizar yawon bu\u0257e ido, amma yana da kyau ku san cewa bizar gajeren zango ba ta ta\u0199aitu a iya bizar yawon bu\u0257e ido ba, akwai wasu nau&#8217;o&#8217;in biza da su ma na gajeren zango ne kamar:<\/p>\r\n<ul style=\"text-align: justify;\">\r\n\t<li><strong>Transit:<\/strong> izinin gajeren zango ne (<strong>tsanani awa 24<\/strong>) domin wucewa ta iyakar \u0199asa, ruwa ko ta sama ta wata \u0199asa.<\/li>\r\n\t<li><strong>Tourism:<\/strong> Ana amfani da ita wurin yawon sha\u0199atawa da zama na \u0257an gajeren lokaci a wata \u0199asar. Haka ana iya amfani da ita wajen yin wasu \u0199ananan abubuwa irinsu ziyarar \u01b4an&#8217;uwa da abokan arziki, halartar tarukan kasuwanci ko na karatu na gajeren lokaci.<\/li>\r\n<\/ul>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Su kuma bizojin dogon zango ga su kamar haka:<\/p>\r\n<ul style=\"text-align: justify;\">\r\n\t<li><strong>Bizar aiki<\/strong><\/li>\r\n\t<li><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/study-in-iran\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Bizar karatu<\/strong><\/a><\/li>\r\n\t<li><strong>Bizar zama<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Bizar hannun jari<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Bizar kasuwanci<\/strong><\/li>\r\n\t<li><strong>Bizar start-up<\/strong><\/li>\r\n<\/ul>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Wace_irin_biza_muke_bu%C6%99ata\"><\/span>Wace irin biza muke bu\u0199ata?<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Akwai nau&#8217;o&#8217;in biza da dama da ake bayarwa bisa la&#8217;akari da abun da zai kai mutum \u0199asar da zai je. Haka kuma akwai yiwuar shiga wasu \u0199asashen ba tare da biza ba idan ta kama. Misali idan za ka tafi yawon bu\u0257e ido a \u0199asar Turkey na tsawon wata 1 ba ka da bu\u0199atar biza, amma idan aiki za ka je yi ko <a href=\"https:\/\/edutsn.com\/study-in-iran\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">karatu<\/a>, dole ne ka nemi bizar aikin ko <a href=\"https:\/\/edutsn.com\/study-in-iran\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">bizar karatu<\/a> a ofishin jakadancinsu.<\/p>\r\n<ul style=\"text-align: justify;\">\r\n\t<li><strong><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/study-in-iran\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Educational Visa<\/a>:<\/strong> Idan kana son zuwa wata \u0199asa karatu dole ne ka nemi bizar karatu ta wannan \u0199asar.<\/li>\r\n\t<li><strong>Transit Visa:<\/strong> Idan za ka tafi wata \u0199asa amma ba kai-tsaye ba har ya zama cewa za ku \u0257an yi zaman jira a wata \u0199asar a kan hanya, mai yiwuwa ku bu\u0199aci kar\u0253ar wannan nau&#8217;in biza \u0257in wato transit visa.<\/li>\r\n\t<li><strong>Tourist Visa:<\/strong> Idan za ku shiga wata \u0199asa ku \u0257an kwana biyu domin yawatawa, za ku bu\u0199aci wannan nau&#8217;in biza ne.<\/li>\r\n\t<li><strong>Work Visa:<\/strong> Ana iya kar\u0253ar bizar aiki ne kawai idan mutum ya samu gayyatar aiki daga \u0199asar da yake son zuwa.<\/li>\r\n\t<li><strong><a href=\"https:\/\/edutsn.com\/medicine-in-iran\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Medical Visa<\/a>:<\/strong> Ana bayar da ita ne domin marasa lafiyan da za su yi jinya a asibitocin wata \u0199asa.<\/li>\r\n<\/ul>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Domin karbar izinin shiga \u0199asa na gajeren lokaci, kawai ana bu\u0199atar ka za\u0253i lokacin da za ka tafi embassy \u0257in \u0199asar tare da tarjamar takardun da ake bu\u0199ata. Daga nan ka shigar da bu\u0199atar neman biza, da zaran ka kar\u0253i bizar shikenan ka samu izinin shiga \u0199asar da kake son zuwa.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Amma idan za ka jima a \u0199asar ko kuma za ka zauna can ne gaba\u0257aya a madadin tafiyar gajeren zango, dole ne ka za\u0253i bizar dogon zango sannan baya ga abubuwan da muka ambata a sama, dole a nemi \u0199arin wasu mihimman takardu.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Misali, idan kana son tafiya karatu na dogon zango ne a \u0199asashe irin Canada, kafin biza dole ne ka fara neman takardar makaranta (admission letter) tare da sauran takardun da ke da ala\u0199a dahadafin tafiyarka irinsu cv, transcript, language certificate, da sauransu wanda za a nuna a embassy da makarantar da za a je.<\/p>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Ta_yaya_za_mu_kar%C9%93i_biza\"><\/span>Ta yaya za mu kar\u0253i biza?<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Dole ne a tura bu\u0199atar kar\u0253ar biza da farko kafin a yi maganan kar\u0253a. Ana iya neman biza ta hanyar zuwa embassy ko ta hanyar aike, hatta ta online a wasu lokutan. Ana buga biza a matsayin stika ko stamp a jikin fasfo. Ana kuma iya bada ita a matsayin takarda mai zaman kanta ko kuma a tura ta na&#8217;ura, amma idan ta na&#8217;ura ne dole a yi printing a ri\u0199e a hannu yayin shiga \u0199asar da za a tafi.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Wasu \u0199asashe (irin \u0199asashen da ke yankin Schengen) na da yarjejeniya a tsakaninsu cewa za su ba \u01b4an \u0199asarsu damar shiga \u0199asashen juna ba tare da biza ba. Majalisar kula da yawon bu\u0257e ido ta duniya ta sanar da cewa yawan masu yawon bu\u0257e ido da ke bu\u0199atar biza kafin tafiya zai ragu sannu a hankali nan da \u01b4an shekaru masu zuwa.<\/p>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Minene_sharu%C9%97an_kar%C9%93ar_biza\"><\/span>Minene sharu\u0257an kar\u0253ar biza?<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Wata bizar ba ta bu\u0199atar sai mutum ya je da kansa, wata kuma mutum ya tafi ofishin immigration ko ofishin jakadancin \u0199asar da za shi kafin lokacin tafiyarsa. Wanann ya sa da yawan mutane ke dam\u0199a process \u0257in kar\u0253ar bizarsu a hannun kamfanonin da ke da \u0199warewa a wannan fannin. Wa\u0257annan kamfanoni na da lasisin yi ma matafiya biza daga ofisoshin jakadancin \u0199asashe.<\/p>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Wasu_irin_mutane_ake_hana_ma_biza\"><\/span>Wasu irin mutane ake hana ma biza?<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Wasu \u0199asashe kan hana biza ga mutanen da ke \u0257auke da wasu nau&#8217;o&#8217;in cuta na musamman irin cutar \u0199anjamau, dukda shi ma wannan ya dogara da nau&#8217;in bizar da ake son kar\u0253a. Hakazalika masu bada biza suna duba record \u0257in wanda za a bawa idan bai ta\u0253a aikata laifuka a baya ba, ko kuma idan bai ta\u0253a yin mu&#8217;amalolin da suka sa\u0253a doka ba kafin su bari ya shiga \u0199asarsu. Haka kuma akwai \u0199asashen da ke hana biza ga mutanen da suka zo daga \u0199asar da suke da rashin jituwa ko \u0199iyayya da ita.<\/p>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Matakan_kar%C9%93ar_biza\"><\/span>Matakan kar\u0253ar biza<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Matakai da dokokin kar\u0253ar biza sun dogara ne da \u0199asar da mutum zai tafi. Akwai \u0199asashen da basu da ofishin jakadanci a Iran. Wannan ya sa dole sai an je wata ma\u0199ociyar \u0199asa domin yin wasu ayyukan da suka shafi kar\u0253ar biza irin thumbprint da sauransu. Ana iya bin matakan kar\u0253ar biza na \u0199asashe da yawa irinsu Canada, Schengen, Australia, England, da sauransu a shafin yanar gizo na visaland.<\/p>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Me_yasa_sai_an_zabi_lokacin_zuwa_embassy\"><\/span>Me yasa sai an zabi lokacin zuwa embassy?<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Bisa la&#8217;akari da nau&#8217;in bizar da kuke so, dole ku bada takardun da ake bu\u0199ata a embassy sannan ku yi interview da ma&#8217;aikatan. Bayan bayar da takardu ana komawa domin yin thumbprint. Amma sakamakon yawan masu zuwa neman biza, wasu ofisoshin jakadancin na yin wani tsari na ayyana lokacin da kowa zai dawo domin gujewa cinkoson jama&#8217;a.<\/p>\r\n<h2 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Farashin_kar%C9%93ar_biza\"><\/span>Farashin kar\u0253ar biza<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Ku\u0257in biza sun dogara da \u0199asa da kuma nau&#8217;in bizar da ake so a kar\u0253a. Ku\u0257in sun \u0199unshi ku\u0257a\u0257en duka ayyukan da ake yi na bizar a dun\u0199ule, ayyuka irinsu thubmprint, tantance takardu, da sauransu. Ku\u0257in biza sun bambanta tsakanin \u0199asashe, ta yiwu ma ba sai an biya ku\u0257in wasu abubuwan ba a wata \u0199asar.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Adireshin shafukan ofisoshin jakadanci na wasu \u0199asashe:<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\"><a href=\"https:\/\/mfa.gov.ir\/portal\/viewpage\/15141\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Shafin ofisoshin jakadancin \u0199asar Iran<\/a><\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\"><a href=\"https:\/\/mofa.gov.iq\/%d8%a7%d9%84%d8%a8%d8%b9%d8%ab%d8%a7%d8%aa-%d8%a7%d9%84%d8%b9%d8%b1%d8%a7%d9%82%d9%8a%d8%a9-%d9%81%d9%8a-%d8%a7%d9%84%d8%ae%d8%a7%d8%b1%d8%ac\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Shafin ofisoshin jakadancin \u0199asar Iraq<\/a><\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\"><a href=\"https:\/\/mfa.gov.af\/fa\/farsi-home\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Shafin ofishin harkokin waje na \u0199asar Afghanistan<\/a><\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\"><a href=\"https:\/\/mofa.gov.pk\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Shafin ofishin harkokin waje na \u0199asar Pakistan<\/a><\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\"><a href=\"https:\/\/www.mofa-ye.org\/Pages\/%d8%a7%d9%84%d8%a8%d8%b9%d8%ab%d8%a7%d8%aa-%d8%a7%d9%84%d8%af%d8%a8%d9%84%d9%88%d9%85%d8%a7%d8%b3%d9%8a%d8%a9-%d8%a7%d9%84%d9%8a%d9%85%d9%86%d9%8a%d8%a9-%d9%81%d9%8a-%d8%a7%d9%84%d8%ae%d8%a7%d8%b1\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Shafin ofisoshin jakadancin \u0199asar Yemen<\/a><\/p>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_51262\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"51262\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>Idan kuna bu\u0199atar amsoshin tambayoyi kamar; minene biza da fasfo, minene bambancin biza da fasfo, kashe-kashen biza, kashe-kashen fasfo, ku kasance tare da mu. A halin yanzu, sabbin bayanan \u0199ididdiga na nuna cewa akwai \u0199asashe 195 mabambanta a doron duniya&#8230;","protected":false},"author":165,"featured_media":47304,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[1056,981,972],"tags":[1057],"class_list":["post-51262","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fitattun-labarai","category-labarai","category-shafi","tag-iran-hau"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/51262","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/users\/165"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=51262"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/51262\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/47304"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=51262"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=51262"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=51262"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}