{"id":51991,"date":"2024-06-11T17:55:53","date_gmt":"2024-06-11T14:25:53","guid":{"rendered":"https:\/\/edutsn.com\/karatu-a-jamioi-masu-sau%c6%99in-ku%c9%97i\/"},"modified":"2024-12-19T16:31:47","modified_gmt":"2024-12-19T13:01:47","slug":"karatu-a-jamioi-masu-sau%c6%99in-ku%c9%97i","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/karatu-a-jamioi-masu-sau%c6%99in-ku%c9%97i\/","title":{"rendered":"Karatu a jami&#8217;o&#8217;i masu sau\u0199in ku\u0257i"},"content":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_51991\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"51991\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" =0 title=\"\"><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div><p>Wannan rubutun ya shafi karatu a jami&#8217;o&#8217;i masu kyau kuma masu sau\u0199in ku\u0257i a Iran ga \u0257aliban waje. A cigaban rubutun mun yi \u0199o\u0199arin kawo wa\u0257annan jami&#8217;o&#8217;i, hakan zai sau\u0199a\u0199e muku za\u0253inku game da <a href=\"https:\/\/edutsn.com\/ferdowsi-university\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Karatu a Iran<\/a>.<\/p>\r\n<h2><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Karatu_a_jamioi_masu_sau%C6%99in_ku%C9%97i_a_Iran\"><\/span>Karatu a jami&#8217;o&#8217;i masu sau\u0199in ku\u0257i a Iran<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h2>\r\n<p>Fita waje karatu \u0257aya ne daga cikin abubuwan da ke yin tasiri a goben mutum. Saboda muhimmancin hakan ne ya sa yana da kyau kafin mutum ya yi bincike sosai game da \u0199asar da yake son zuwa karatu. Zamaninnan \u0199asashe na fuskantar kai-komo na mutane masu yawa tsakaninsu saboda mabambantan dalilai da suka ha\u0257a da karatu, aiki, samun walwala, ko kuma gudun hijira saboda ya\u0199i ko matsalolin siyasa, da dai sauransu.<br \/>\r\n\u018aaya daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi karatu shi ne za\u0253en makaranta wanda hakan na iya dogara da yanayin tsadar makarantar. Ana sanar da ku\u0257in makaranta ga \u0257aliban waje kamar yadda makarantun suka saka. A cigaba, za mu kawo sunan jami&#8217;a tare da ku\u0257in makarantarta.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Al-Zahra_University\"><\/span>Al-Zahra University<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>An assasa Jami&#8217;ar Al-Zahra (AS) a shekarar 1952 a arewa maso yammacin garin <a href=\"https:\/\/edutsn.com\/tehran\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Tehran<\/a> bisa hadafin ilmantar da \u0257alibai mata a matakin jami&#8217;a, inda bayan nasarar juyin juya hali na Iran jami&#8217;ar ta ci gaba da bun\u0199asa ta \u0253angarori daban-daban. Manufar assasa jami&#8217;ar ita ce tarbiyantar da mata a ilmance da al&#8217;adance wa\u0257anda bayan kula da iyali, za su iya taka rawa a \u0253angare zamantakewar al&#8217;umma, siyasa, al&#8217;adu, da tattalin arzikin \u0199asa. Yanzu haka a jami&#8217;ar akwai \u0257alibai 0279 masu karatu a \u0199ar\u0199ashin kulawar ma&#8217;aikatan tsangayar ilimi 129 a sassan koyarwa 33 \u0257auke da kwasa-kwasai 33 a matakan digiri, masters, da PhD a cikin makarantu 33. Kusan kashi 2 bisa 3 na malaman wannan jami&#8217;a mata ne. Kashi 31% daga cikin membobin tsangayar ilimi sun kai matakin professor, kashi 11% na matakin associate professor, sai kashi 19 masu assistant professor. A kowace shekara ana wallafa dubban ma\u0199aloli da gomman littafai daga ayyukan bincike na \u0257alibai da malaman jami&#8217;ar a matakin cikin gida da matakin \u0199asa da \u0199asa. Jami&#8217;ar Al Zahra na daga cikin jami&#8217;o&#8217;i masu sau\u0199in ku\u0257i a Iran kuma tana da kayan aiki na koyarwa, bincike, al&#8217;adu, da wasanni a cikin farfajiyarta mai kyau, mai girman fiye da hekta 33 a cikin Tehran da reshenta na garin Urmia. Jami&#8217;ar ta tanadi duka irin kayan aikin da ake bu\u0199ata domin bun\u0199asa ilimin \u0257alibanta.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"University_of_Birjand\"><\/span>University of Birjand<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>Jami&#8217;ar Birjand ita ce ginshi\u0199in ilimi da karatu a gabacin \u0199asar Iran, kuma ita ce cibiyar koyarwa mafi da\u0257ewa a lardin Khorasan Junubi, tana da tarihin sama da shekaru <span lang=\"fa\" xml:lang=\"fa\">46<\/span> a fannin karatu, al&#8217;adu da zamantakewa.inda ta horar da \u0199wararrun ma&#8217;aikata 30,000. Jami&#8217;ar ta cika duka sharu\u0257an da ya kamata ace jami&#8217;a na da su kuma tana da tsayayyun membobin kwamitin amintattu da kwamitin bincike na musamman. Jami&#8217;ar Birjand na da kimanin \u0257alibai 13,000 a masu karatun kwasa-kwasai 340 a matakan associate degree, B.Sc, M.Sc, da PhD. \u018aaliban da ke karatu a matakin postgraduate a wannan jami&#8217;ar za su kai kashi 30 bisa \u0257ari na duka \u0257aliban jami&#8217;ar. Jami&#8217;ar na da ma&#8217;aikatan tsangayar ilimi guda 350 kuma tana \u0257aya daga cikin jami&#8217;o&#8217;i masu sau\u0199in ku\u0257i a lardin Khorasan Junubi na \u0199asar Iran. Jami&#8217;ar na da ma&#8217;aikata 350 a \u0253angarori daban-daban na jami&#8217;ar irinsu ofisoshi, ayyukan da suka shafi karatun \u0257alibai, walwalar \u0257alibai, da sauran sassa. Jami&#8217;ar na da kwalejoji 11 a harabobi 3 na Shokat Abad, Amir Abad, da Shohada. Makarantun sun ha\u0257a da; Kwalejin Science, Agriculture, Engineering, Literature and Human Science, Art, Sport Science, Educational Sciences and Psychology, Mathematical Sciences and Statistics, Natural Resources and Enviroment, Kwalejin Electrical and Computer, da kwalejin Technical.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Ahlul_Bayt_International_University\"><\/span>Ahlul Bayt International University<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>An assasa jami&#8217;ar &#8220;Ahlul Bayt (AS) International University&#8221; a shekarar 2004 bisa hadafin taimakawa wajen bun\u0199asa ilimi da samar da abubuwan bu\u0199atun ilimi da na bincike domin amfanin \u0257alibai da masu bincike musulmai da kuma taimakawa wajen sanin al&#8217;adu da wayewar musulunci, a matakan karatu na postgraduate a wani \u0199aramin muhalli kafin ta koma cikakkiyar jami&#8217;a a shekarar 2011. Jami&#8217;ar na nan a wani kyakkyawan muhalli a garin Tehran wato babban birin tarayya na \u0199asar Iran, kuma tana da \u0199wararrun ma&#8217;aikatan tsangayar ilimi a mabambantan kwasa-kwasai, sannan tana daga cikin jami&#8217;o&#8217;i masu sau\u0199in ku\u0257i a Iran \u0257auke da \u0257alibai masu yawa daga mabambantan \u0199asashe kuma har yanzu tana da shau\u0199in kar\u0253ar \u0257alibai daga ko&#8217;ina a fa\u0257in duniya. Hakazalika wannan jami&#8217;a na alfahari da cewa tana cikin \u0199ungiyar jami&#8217;o&#8217;in \u0199asa da \u0199asa a \u0199ar\u0199ashin ma&#8217;aikatar <a href=\"https:\/\/www.unesco.org\/en\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">UNESCO<\/a> sannan baya ga karatu, a kowace shekara tana kar\u0253ar ba\u0199uncin malamai da masu bincike domin samar da damar bincike a sassa daban-daban na duniya.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Persian_Gulf_University\"><\/span>Persian Gulf University<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>Jami&#8217;ar Khalije Fars jami&#8217;ar gwamnati ce da ke \u0199ar\u0199ashin kulawar ma&#8217;aikatar ilimi da binciken ta Iran, ita ce cibiyar koyarwa mafi girma a lardin Bushehr kuma tana cikin garin Bushehr ne. Jami&#8217;ar ta fara aiki ne da sunan &#8220;Jami&#8217;ar Bushehr&#8221; da kwasa-kwasai biyu kacal na Civil Engineering da Mechanical Engineering a shekarar 1992. Jami&#8217;ar Khalije Fars na da cibiyoyin bincike guda 9 da kwaleji guda 8 kamar haka; kwalejin literature and human science, kwalejin business, nanoscience and technology, agriculture, engineering, smart systems engineering and data science, art and architecture, kwalejin petroleum engineering, gas and petrochemical, marine science and technology, da kwalejin mass engineering. Hakazalika jami&#8217;ar na da ofisoshin al&#8217;amuran koyarwa 5, al&#8217;adu da al&#8217;amuran \u0257alibai, bincike da fasaha, tsari da bun\u0199asawa, da albarkatun \u0257an&#8217;adam. Yanzu haka ana yin kwasa-kwasai 99 a jami&#8217;ar wanda daga cikinsu, 31 na digiri ne, 56 na masters, 13 kuma na PhD.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Sajjad_University_of_Technology\"><\/span>Sajjad University of Technology<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p><span lang=\"hi-IN\" xml:lang=\"hi-IN\">J<\/span><span lang=\"hi-IN\" xml:lang=\"hi-IN\">ami&#8217;ar Fasaha ta Sajjad ta fara ayyukanta na koyarwa ne a shekarar 1995 a garin Mashhad a matsayin cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare bayan ta kar\u0253i lasisi daga majalisar bun\u0199asa karatun gaba da sakandare da ke ma&#8217;aikatar ilimi da bincike.<\/span> <span lang=\"hi-IN\" xml:lang=\"hi-IN\">Binciken ma&#8217;aikatar ilimi ya nuna cewa a koyaushe wannan jami&#8217;ar ta kasance a sahun gaba a cikin jami&#8217;o&#8217;in da ba na gwamnati ba na \u0199asar.<\/span> <span lang=\"hi-IN\" xml:lang=\"hi-IN\">Bayanan \u0199ididdiga na ma&#8217;aikatar SANJESH sun nuna cewa a shekaru 5 da suka gabata, an samu kimanin \u0257alibai 3500 da suka ci jarabawar \u0199asa ta zuwa matakin masters daga wannan jami&#8217;a, hakazalika akwai \u0257aliban da aka yaye daga jami&#8217;ar fasaha ta Sajjad da yawa a sassa daban-daban na masana&#8217;antun \u0199asar, wannan ma babbar nasara ce ga jami&#8217;ar.<\/span><br \/>\r\n<span lang=\"hi-IN\" xml:lang=\"hi-IN\">Jami&#8217;ar Sajjad na gabatar da ayyukan koyarwa a duka sassan karatu na digiri, mastas, da PhD sannan binike ya nuna cewa bayan <a href=\"https:\/\/edutsn.com\/ferdowsi-university\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">jami&#8217;ar Ferdowsi<\/a>, wannan jami&#8217;a ta fi kowace jami&#8217;a a garin Mashhad yawan \u0257alibai da ke shau\u0199in yin karatu a cikinta.<\/span><span lang=\"hi-IN\" xml:lang=\"hi-IN\">Kwamitin assasa jami&#8217;ar ya \u0199unshi malaman jami&#8217;a da wasu jiga-jigai daga masana&#8217;antun \u0199asar Iran.<\/span> <span lang=\"hi-IN\" xml:lang=\"hi-IN\">Jami&#8217;ar Sajjad ita ce jami&#8217;ar farko a \u0199asar Iran wadda aka samar daga cibiyar bincike ta masana&#8217;anta. <\/span><\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"International_University_Of_Chabahar\"><\/span>International University Of Chabahar<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>Jami&#8217;ar \u0199asa da \u0199asa ta Chabahar ta fara aiki shekarar 2002 inda ta kar\u0253i \u0257alibai a kwasa-kwasai 8 tare da ha\u0257in gwiwar jami&#8217;ar London, inda akan yi jarabawoyin \u0199arshen shekara a jami&#8217;ar Chabahar amma jami&#8217;ar London ce ke bada shaidar kammala karatu, daga bisani jami&#8217;ar ta Chabahar ta dam\u0199a ma \u0257alibanta. A shekarar 2009 wannan jami&#8217;a ta fara kar\u0253ar \u0257alibai ta hanyar jarabawar shiga jami&#8217;a ta \u0199asa bayan ta bun\u0199asa yawan kwasa-kwasanta a matakan digiri. Yanzu haka a wannan jami&#8217;a ana yin kwasa-kwasai sama da guda ashirin a matakin digiri da mastas.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"University_of_Neyshabur\"><\/span>University of Neyshabur<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>Jami&#8217;ar Neyshabur na amfani da sabbin fasahar gudanarwa, fasahar koyarwa da bincike, \u0199arfafawa, da jajircewar ma&#8217;aikatanta na tsangayar ilimi da sauran ma&#8217;aikata domin tarbiyyantar da \u0199wararrun ma&#8217;aikata da \u01b4ankasuwa, tare da bun\u0199asa ilimi da al&#8217;adun \u0199asar. A halin yanzu jami&#8217;ar Neyshabur na da kwaleji guda hu\u0257u; Art, Human Science, Basic Science, da kwalejin Technical and Engineering. Jimillar girman wannan jami&#8217;a ya haura murabba&#8217;in mita 15730.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Qom_University_of_Technology\"><\/span>Qom University of Technology<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>Jami&#8217;ar fasaha ta Qom ta fara aiki a shekarar 2008 da kwasa-kwasai 2 na Industrial Engineering da Computer Engineering da nufin horar da \u0257alibai masu himma da addini. Yanzu jami&#8217;ar na da makarantu 3; Technical and Engineering, Electrical and Computer Engineering, da Basic Science kuma tana da kwasa-kwasai 23 a matakin digiri da mastas, tana da membobin tsangayar ilimi 57 da \u0257alibai 2000 daga sassa daban-daban na Iran musamman daga lardin Tehran da Qom. Ana fatan cewa \u0257aliban da suka yi karatu a wannan jami&#8217;a su shiga sahun \u0199wararrun injiniyoyi da masana kimiyya na \u0199asar. Hakazalika jami&#8217;ar na daga cikin jami&#8217;o&#8217;in fasaha da suka dace da \u0257aliban waje, sannan tana cikin jami&#8217;o&#8217;i masu sau\u0199in ku\u0257i a Iran.<\/p>\r\n<h3><span class=\"ez-toc-section\" id=\"University_of_Bojnord\"><\/span>University of Bojnord<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p>Jami&#8217;ar Bojnord jami&#8217;a ce ta gwamnati wadda aka assasa a garin Bojnord a shekarar 2005. Yanzu haka akwai \u0257alibai sama da 12000 masu karatu a jami&#8217;ar. Ana kallon jami&#8217;ar a matsayin ita ce jami&#8217;ar asali ta Khorasan Junubi. Rahoton hul\u0257a da jama&#8217;a na jami&#8217;ar Bojnord ya bayyana cewa cibiyar bada shawara ga \u0257alibai ta wannan jami&#8217;ar ta samu kyautar matsayi na farko karo na 4 a jere, a bukin tattara shugabanni da ma&#8217;aikatan cibiyoyin bada shawara na \u0199asa.<\/p>\r\n<p>Rahoton ya nuna cewa an gudanar da binciken ne a fannin ayyukan lafiyar \u0199wa\u0199walwa da zamantakewar \u0257alibai a kwanakin corona a shekarar 2020, inda aka gabatar da lambar yabo ta musamman daga hukumar lafiya da ma&#8217;aikatar ilimi zuwa ga wannan cibiyar. Dukda cewa jami&#8217;ar ita ce ta \u0257aya a lardin Khorasan Junubi, tana \u0257aya daga cikin jami&#8217;o&#8217;i masu sau\u0199in ku\u0257i ga \u0257aliban \u0199asashen waje.<\/p>\r\n<p>Jami&#8217;o&#8217;in da muka ambata suna daga cikin jami&#8217;o&#8217;in iran masu kyau wa\u0257anda basu da tsada kuma suna kar\u0253ar \u0257alibai daga mabambantan \u0199asashe a kowace shekara. A kodayaushe kamfaninmu na \u0199o\u0199arin ganin cewa ya tattara muku muhimman bayanai game da jami&#8217;o&#8217;in \u0199asar Iran.<\/p>\r\n<p>&nbsp;<\/p>\r\n<p>&nbsp;<\/p>\r\n<p>&nbsp;<\/p>\r\n<p>&nbsp;<\/p>\r\n<p>&nbsp;<\/p>\r\n<p>&nbsp;<\/p>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_51991\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"51991\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>Wannan rubutun ya shafi karatu a jami&#8217;o&#8217;i masu kyau kuma masu sau\u0199in ku\u0257i a Iran ga \u0257aliban waje. A cigaban rubutun mun yi \u0199o\u0199arin kawo wa\u0257annan jami&#8217;o&#8217;i, hakan zai sau\u0199a\u0199e muku za\u0253inku game da Karatu a Iran. Karatu a jami&#8217;o&#8217;i&#8230;","protected":false},"author":127,"featured_media":50705,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[972,1117],"tags":[],"class_list":["post-51991","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-shafi","category----hau"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/51991","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/users\/127"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=51991"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/51991\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/50705"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=51991"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=51991"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=51991"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}