{"id":59713,"date":"2024-10-16T17:30:08","date_gmt":"2024-10-16T14:00:08","guid":{"rendered":"https:\/\/edutsn.com\/?p=59713"},"modified":"2024-12-19T14:28:26","modified_gmt":"2024-12-19T10:58:26","slug":"karatu-a-iran-university-of-art","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/karatu-a-iran-university-of-art\/","title":{"rendered":"Karatu a Iran University of Art"},"content":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_59713\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"59713\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" =0 title=\"\"><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div><p style=\"text-align: justify;\">Jami&#8217;ar Fasahar Zane-Zane ta Iran (Iran University of Art) ita ce makarantar gaba da sakandare mafi girma a fannonin da suka shafi art a birnin <a href=\"https:\/\/edutsn.com\/en\/study-in-tehran\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Tehran<\/a>. An samar da ita ne ta hanyar ha\u0257e makarantu biyar na art na gabanin juyin musulunci na Iran (makarantun Farabi University, Decorative Arts College, Dramatic Arts College, Higher Music School, da National Music Academy). A wannan rubutun, mu kawo muku wadataccen bayani game da yanayin karatu a wannan jami&#8217;a mai suna Iran University of Art.\u00a0<\/p>\r\n<h3 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Gabatarwa\"><\/span>Gabatarwa<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Iran University of Art jami&#8217;a ce da ta ke\u0253anci fannonin zane-zane wato art. An assasa ta a shekarar 1979 bayan ha\u0257e makarantu guda biyar na art kamar haka; Farabi University, Decorative Arts Academy, Dramatic Arts College, Higher Music School, and National Music Academy.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Daga cikin wa\u0257annan makarantun da aka ha\u0257e, Higher Music School ita ce mafi da\u0257ewa. Ta tsaya da \u0199afafuwanta ne bayan an ware ta daga Darul Funun a shekarar 1918 a matsayin ajin koyar da wa\u0199e. Gholamreza Minbashian, shi ne wanda ya ci gaba da tafiyar da ita tare da taimakon \u0257ansa Nasr al-Sultan a \u0199ar\u0199ashin kulawar ma&#8217;aikatariIlimi, shi ne ya sanya mata suna &#8220;Music School&#8221;.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Bayan nasarar juyin musulunci, domin cimma manufofin al&#8217;adu da na fasahar zane-zane na al&#8217;ummar musulmi da bun\u0199asa fasahohin zane musamman na musulunci da na gargajiya, tare da ilmantar da wa\u0257annan \u0199wararrun game da tsofaffin al\u2019adun Iran, musulunci, da na duniya, kafa wata cibiya ta karatun gaba da sakandare a fannin art ya shiga cikin \u0199udurin ma&#8217;aikatara ilimin kimiyya. A domin haka ha\u0257e wa\u0257annan makarantun guda 5 na kafin juyin juya hali, aka assasa wannan jami&#8217;a ta fasahar zane-zane a shekarar 1979, inda ta fara aiki a hukumance shekarar 1983.<\/p>\r\n<h3 dir=\"rtl\" style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"atu\"><\/span>atu<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<h3 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Ku%C9%97in_Makarantar_Iran_University_of_Art\"><\/span>Ku\u0257in Makarantar Iran University of Art<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<h3 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Makarantu\"><\/span>Makarantu<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<h4 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Makarantar_Applied_Arts\"><\/span>Makarantar Applied Arts<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">An kafa wannan kwalejin a shekarar 1960 ta hannun majalisar al&#8217;adu da fasaha ta lokacin. Asasin karatu a kwalejin ya ginu ne a kan manufar muhimmantar da ilimin fasahar zane-zane tare da la&#8217;akari da al&#8217;adun \u0199asar. Saboda haka ne aka fi bada \u0199arfi a fannoni irin su textile weaving and printing, decorative painting, ceramics (pottery), visual communication, interior architecture, da sauransu. Tun bayan canja sunan jami&#8217;ar zuwa &#8220;Iran University of Art&#8221;, kwalejin na Applied Arts ya ci gaba da gudanar da ayyukansa da kwasa-kwasai guda uku na Industrial Design, Handicrafts, da Music, a matakin Bachelor&#8217;s Degree.<\/p>\r\n<h4 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Kwalejin_Visual_Arts\"><\/span>Kwalejin Visual Arts<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Wannan kwalejin na Visual Arts an assasa shi ne a shekarar 1978 a cikin kamfushin jami&#8217;ar ta Iran University of Art, sannan aka dawo da wasu sassan koyarwa da ke \u0199ar\u0199ashin kwalejin Decorative Arts na jami&#8217;ar Farabi zuwa wannan kwalejin. A shekarar 1982, kwalejin ya fara kar\u0253ar \u0257aliban makarantun da aka ha\u0257e aka assasa wannan jami&#8217;a, wa\u0257anda suka saura da abunda bai wuce unit 25 su kammala karatunsu ba. Tun daga shekarar 1983 wannan kwalejin ya ci gaba da koyar da kwasa-kwasai uku na Photography, Painting, da Visual Communication a matakin undergraduate.<\/p>\r\n<h4 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Kwalejin_Cinema_and_Theater\"><\/span>Kwalejin Cinema and Theater<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">A shekarar 1957 ne daraktan \u0199oli na Fine Arts ya bayar da lasisin assasa department \u0257in Dramatic Arts. An assasa makarantar ta Dramatic Arts a shekarar 1964 bayan amincewar majalisar al&#8217;adu da fasahar zane ta \u0199asa. Manufar wannan makaranta ita ce horar da mutane masu basira a duka fannonin Theater, fannonin da suka ha\u0257a da rubutu, bada umarni, wasan kwaikwayo, kwalliya, da shirya dandali. A hankali aka shigar da sassan koyarwa na Cinema da Television a wannan kwalejin, a shekarar 1970 kuma aka canja masa suna zuwa &#8220;Kwalejin Dramatic Arts&#8221; inda ya ci gaba da gudanar da ayyukansa.<\/p>\r\n<h4 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Kwalejin_Music\"><\/span>Kwalejin Music<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Bayan ha\u0257e wa\u0257annan manyan makarantun, ciki har da Music High School (1959) da Music Academy (1971) inda aka samar da jami&#8217;ar fasahar zane ta Iran, an fara kwas \u0257in Music ne a shekarar 1989 a \u0199ar\u0199ashin kwalejin Applied Arts. Bayan samun izini daga majalisar bun\u0199asa karatun gaba da sakandare a shekarar 1994 ne aka bu\u0257e kwalejin Music a matsayin kwaleji na farko (da ke \u0199ar\u0199ashin jami&#8217;a) a \u0199asar Iran, inda aka fara da kwas biyu na Music da Military Music, a matakin undergraduate. Kwalejin na nan cikin harabar Karaj ta jami&#8217;ar.<\/p>\r\n<h4 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Makarantar_Architecture_and_Urban_Planning\"><\/span>Makarantar Architecture and Urban Planning<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Kwalejin Architecture da Urban Planning ta Iran University of Art ta fara ayyukanta a shekarar 1999 ta hanyar kar\u0253ar \u0257aliban undergraduate a fannin Urban Planning, sannan a shekarar 2000 a fannin Architecture. Kwalejin tana da yalwar murabba&#8217;in mita 2,600 a harabar Karaj. Bayan bun\u0199asar kwalejin, an fara kar\u0253ar \u0257aliban graduate a fannin Architecture, a shekarar 2004 kenan, sai kuma Interior Architecture a shekarar 2005.<\/p>\r\n<h4 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Kwalejin_Dramatic_Arts\"><\/span>Kwalejin Dramatic Arts<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Ganin muhimmancin fasahar kwaikwayo (dramatic arts) a wajen gina tunanin matasa, tushen al&#8217;adu da zamantakewar al&#8217;umma, da kuma bu\u0199atar ci gaban gaggawa\u00a0 a fannin wasan kwaikwayo, fina-finai, talabijin, da rediyo, tsohuwar Ma&#8217;aikatar Al&#8217;adu da Fasaha ta kafa babbar makaranta domin horar da &#8216;yan wasan kwaikwayo da masu bincike a wa\u0257annan fannoni. An kafa Sashen Dramatic Arts a shekarar 1957 ta hannun Hukumar Kula da Fasaha ta Fine Arts, \u0199ar\u0199ashin jagorancin Dr. Mehdi Forough.<\/p>\r\n<h4 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Kwalejin_Decorative_Arts\"><\/span>Kwalejin Decorative Arts<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">An kafa wannan kwalejin ne a shekarar 1960 lokacin da aka \u0199ir\u0199iri makarantar Fine Arts Academy, \u0199ar\u0199ashin Ma&#8217;aikatar Al&#8217;adu da Fasaha. An kafa makarantar ne a matsayin tanadi ga bu\u0199atun ilimi na \u0257aliban fasaha da sauran wa\u0257anda ke sha&#8217;awar ci gaba da karatu a fannin na fasaha, da kuma taskacewa da ha\u0253aka sauran fasahohi masu ala\u0199a da fannin.<\/p>\r\n<h4 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Makarantar_Conservation_and_Restoration\"><\/span>Makarantar Conservation and Restoration<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">An fara karatun digirin master&#8217;s a fannin Kula da Gine-gine da Kayan Tarihi (Conservation of Historic Buildings and Cultural Objects) a jami&#8217;ar Iran University of Art a shekarar 1976, wanda ya zama wani muhimmin mataki a tarihin karatun gaba da sakandare a wannan fannin a \u0199asar Iran. A shekarar 1977, an sanya hannu a yarjejeniyar ilimi tsakanin Dr. Jamshid Behnam, shugaban Farabi University a lokacin, da Nosratollah Mojtabai, daraktan gudanarwa na Hukumar Kula da Kayan Tarihi ta \u0199asa, domin samar da ma&#8217;aikatan fasaha da \u0199wararru. Wannan ne mafarin kar\u0253ar \u0257alibai a matakin master&#8217;s na kwas \u0257in Conservation a Farabi University (Iran University of Art ta yanzu).<\/p>\r\n<h4 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Makarantar_Theoretical_Sciences_and_Advanced_Art_Studies\"><\/span>Makarantar Theoretical Sciences and Advanced Art Studies<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h4>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Girman da zurfin muhawarorin fasahar zane, da mahimmancinsu a zamanin yanzu tare da \u0199arin bu\u0199atar gudanar da bincike da karatu mai zurfi kan fasahar Iran da ta duniya, dangantakar addini, al&#8217;adu da fasaha, \u0199o\u0199arin shawo kan \u0199alubalen falsafa a fannin fasaha, da kuma rawar da Iran University of Art take takawa a matsayin cibiyar ilimin fasaha mafi girma a Gabas ta Tsakiya, su suka haifar da kafuwar wannan kwalejin na Theoretical Sciences and Advanced Art Studies a watan May na shekarar 2015, tare da shiri wanda ya \u0199unshi manufofi, dabaru, da hanyoyin aiki na musamman.<\/p>\r\n<h3 dir=\"rtl\" style=\"text-align: justify;\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-56949 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-3.jpg\" alt=\"Faculties of Iran University of Art\" width=\"700\" height=\"700\" title=\"\" srcset=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-3.jpg 700w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-3-300x300.jpg 300w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-3-150x150.jpg 150w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-3-400x400.jpg 400w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-3-75x75.jpg 75w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-3-460x460.jpg 460w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-3-24x24.jpg 24w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-3-36x36.jpg 36w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-3-48x48.jpg 48w\" sizes=\"(max-width: 700px) 100vw, 700px\" \/><\/h3>\r\n<h3 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Kwasa-Kwasai\"><\/span>Kwasa-Kwasai<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<ul style=\"text-align: justify;\">\r\n\t<li>Islamic Art<\/li>\r\n\t<li>World Music Performance &#8211; Guitar<\/li>\r\n\t<li>Iranian Music Performance<\/li>\r\n\t<li>Theater &#8211; Directing<\/li>\r\n\t<li>Puppetry<\/li>\r\n\t<li>Theater &#8211; Acting<\/li>\r\n\t<li>Painting<\/li>\r\n\t<li>Architecture and Energy<\/li>\r\n\t<li>Architectural Engineering<\/li>\r\n\t<li>Architecture<\/li>\r\n\t<li>Museum Studies<\/li>\r\n\t<li>Restoration of Cultural and Historical Objects<\/li>\r\n\t<li>Project and Construction Management<\/li>\r\n\t<li>Carpet &#8211; Restoration and Finishing<\/li>\r\n\t<li>Composition<\/li>\r\n\t<li>Dramatic Literature<\/li>\r\n\t<li>Urban Planning<\/li>\r\n\t<li>Cinema<\/li>\r\n\t<li>Cinema &#8211; Editing<\/li>\r\n\t<li>Cinema &#8211; Cinematography <br \/>\r\nDa sauransu&#8230;<\/li>\r\n<\/ul>\r\n<h3 dir=\"rtl\" style=\"text-align: justify;\"><img decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-56954 size-full\" src=\"https:\/\/edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-4.jpg\" alt=\"Welfare Facilities\" width=\"700\" height=\"700\" title=\"\" srcset=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-4.jpg 700w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-4-300x300.jpg 300w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-4-150x150.jpg 150w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-4-400x400.jpg 400w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-4-75x75.jpg 75w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-4-460x460.jpg 460w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-4-24x24.jpg 24w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-4-36x36.jpg 36w, https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/\u062a\u062d\u0635\u06cc\u0644-\u062f\u0631-\u062f\u0627\u0646\u0634\u06af\u0627\u0647-\u0647\u0646\u0631-\u0627\u06cc\u0631\u0627\u0646-4-48x48.jpg 48w\" sizes=\"(max-width: 700px) 100vw, 700px\" \/><\/h3>\r\n<h3 dir=\"rtl\" style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"i\"><\/span>\u00a0<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<h3 style=\"text-align: justify;\"><span class=\"ez-toc-section\" id=\"Abubuwan_More_Rayuwa\"><\/span>Abubuwan More Rayuwa<span class=\"ez-toc-section-end\"><\/span><\/h3>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">Ana fifita \u0257alibai cikakku (full-time) wa\u0257anda ba mazauna Tehran ba wajen raba \u0257akunan kwana, sai kuma \u0257alibai na wucin gadi (part-time). \u018aaliban da ke harabar makaranta wa\u0257anda ba su sami damar amfani da hostel \u0257in makaranta ba za su iya amfani da hostel masu zaman kansu, masu sau\u0199in farashi. Ana bayar da karin kumallo da abincin dare a hostel, kuma ana rajista ne ta hanyar tsarin abinci da jami&#8217;ar ta tanada. \u018aalibai ne ke za\u0253ar nau&#8217;in abincin da suke so, hakazalika akwai isassun kayan more rayuwa a hostel \u0257in na makaranta.<\/p>\r\n<p style=\"text-align: justify;\">A <a href=\"https:\/\/art.ac.ir\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Iran University of Art<\/a>, an samar da kayan aiki na ilimi ga \u0257alibai a fannoni daban-daban. Wannan ya ha\u0257a da \u0257akunan karatu da \u0257akunan kwamfuta da aka tsara musamman don tallafa wa karatun \u0257alibai. \u018aaliban master&#8217;s a fannin animation na kwalejin Cinema and Theater suna da damar yin amfani da kayan aikin da suka dace da bu\u0199atun karatunsu. Babban laburaren jami&#8217;ar yana da \u0257akin karatu mai kyau da kuma tsarin ba da aron littattafai. Har ila yau, \u0257alibai suna da damar amfani da fitattun \u0257akunan karatu na dijital na duniya, kamar <a href=\"https:\/\/www.ebsco.com\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">EBSCO<\/a>. Bugu da \u0199ari, an samar da intanet mai sauri ga \u0257alibai, sannan akwai damar musayar projects tare da jami&#8217;o&#8217;in \u0199etare masu daraja. Ana fifita \u0257alibai a irin wa\u0257annan ayyukan bisa cancantarsu, ayyukansu, da kuma \u0199warewarsu a harshen Turanci.<\/p>\r\n<p dir=\"rtl\" style=\"text-align: justify;\">\u00a0<\/p>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_59713\" class=\"pvc_stats all  \" data-element-id=\"59713\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg aria-hidden=\"true\" focusable=\"false\" data-prefix=\"far\" data-icon=\"chart-bar\" role=\"img\" xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" viewBox=\"0 0 512 512\" class=\"svg-inline--fa fa-chart-bar fa-w-16 fa-2x\"><path fill=\"currentColor\" d=\"M396.8 352h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V108.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v230.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm-192 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V140.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v198.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zm96 0h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8V204.8c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v134.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8zM496 400H48V80c0-8.84-7.16-16-16-16H16C7.16 64 0 71.16 0 80v336c0 17.67 14.33 32 32 32h464c8.84 0 16-7.16 16-16v-16c0-8.84-7.16-16-16-16zm-387.2-48h22.4c6.4 0 12.8-6.4 12.8-12.8v-70.4c0-6.4-6.4-12.8-12.8-12.8h-22.4c-6.4 0-12.8 6.4-12.8 12.8v70.4c0 6.4 6.4 12.8 12.8 12.8z\" class=\"\"><\/path><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/www.edutsn.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>Jami&#8217;ar Fasahar Zane-Zane ta Iran (Iran University of Art) ita ce makarantar gaba da sakandare mafi girma a fannonin da suka shafi art a birnin Tehran. An samar da ita ne ta hanyar ha\u0257e makarantu biyar na art na gabanin&#8230;","protected":false},"author":69,"featured_media":58879,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[973,974,972],"tags":[],"class_list":["post-59713","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-makarantu","category-makarantun-da-ke-arashin-maaikatar-ilimi","category-shafi"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/59713","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/users\/69"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=59713"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/59713\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/58879"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=59713"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=59713"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/www.edutsn.com\/Hau\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=59713"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}